Abun Al Ajabi
An tura wani Fasto mai shekara 63 da ake kira Luke Eze, gidan yari bayan tuhumar shi da cin zarafin ’yan mata biyu wadanda adda da kanwa suke a jihar Enugu.
Wani Sarki a jihar Osun, Oba Clement Adesuyi Haastrup Ajimoko III, da ke sarautar Ijesa, ya tsige basarake, Busuyi Gbadamosi, bisa zargin satar injunan wuta.
Fitacciyar mai bin addinin gargajiya, Yeye Osunfunmilayo Ajile, ta ce ba za ta bar asalin addinin gargajiya ba duk da barazanar malaman Musulunci a Kwara.
Reno Omokri ya caccaki tsohon dan takarar shugaban kasa a LP a zaben 2023, Peter Obi bayan taya sabon Sarkin Ibadan murnar hawa karagar sarauta a Oyo.
Mawakin siyasa a Najeriya, Dauda Kahutu Rarara ya yi magana kan karrama shi da aka yi da digirin girmamawa da jami’ar European American ta yi a yau Asabar.
Mawakin siyasa a Arewacin Najeriya, Dauda Abdullahi Kahutu Rarara ya samu karramawa ta musamman daga jami'ar European American a birnin tarayya, Abuja.
Wata matar aure, Zuwaira Hassan ta shiga hannu bisa zargin kona al'aurar kanwar mijinta yar shekara 10, ta bayyana cewa ta yi haka ne kan umarnin wata mai magani.
Yayin da ake yada rahoton cewa ministan Abuja, Nyesom Wike ba shi da lafiya, tsohon gwamnan Rivers, ya danganta hakan da siyasa inda ya ce babu abin da ke damunsa.
Wani magidanci, Mista Ishaku Joseph ya maka saurayin diyarsa, Yunana Zock a kotu jam tuhumar kwashe kudin gadon matarsa, wacce ta bar duniya kwanakin baya.
Abun Al Ajabi
Samu kari