Abun Al Ajabi
'Yan sanda sun cafke wata dalibar jami'ar Ekiti bisa zargin yin garkuwa da kanta domin ta sha soyayya da saurayinta. Kwamishinan 'yan sanda ya ce za a kai ta kotu.
Kwamishinar jin dadin mata ta jihar Anambra, Ify Obinabo, ta bayyana yadda wata mata ta zo ofishinta tana neman taimako kan yadda ɗanta ke yi wa mata ciki.
Rahotanni daga Ibadan, jihar Oyo sun tabbatar da rasuwar Baale na Oluyole Estate, Cif Yemi Ogunyemi, da safiyar ranar Laraba, 7 ga watan Mayu, 2025.
Kotun shari'ar Musulunci ta saurari karar mata da miji da aka gurfanar a gabanta bisa zargin auren maza biyu lokaci guda ba tare da saki ba a jihar Kano.
Mutane sun shiga mamaki bayan sace Fasto John Okoriko ya ce babu wani wurin da ake kira aljanna ko wuta, yana mai cewa Allah na kasancewa a zuciyar mai bi.
Bayan shafe wata 4 babu labari, mataimakin gwamnan Taraba, Alhaji Aminu Alkali, ya dawo Jalingo bayan rahoto ya ce ya yi jinya a Abuja da kasar Masar.
Fitaccen matashin dan siyasa, Musa Azare ya ki karɓar mukamin SSA da gwamnan Bauchi ya ba shi, yana mai cewa zai fi amfani idan ya ci gaba da aikinsa na shari’a.
Oluwo na Iwo, Abdulrasheed Akanbi, ya ce Allah kadai ne garkuwarsa, kuma babu wanda zai iya tsige shi ko kashe shi tun bayan hawansa mulki a 2016.
Rahotanni sun ce ɗan Sarki, Al-Waleed bin Khaled bin Talal, wanda ake kira "Sarkin Barci," ya cika shekara 20 bai cikin hayyacinsa bayan hadarin mota a 2005.
Abun Al Ajabi
Samu kari