Abuja
Wani matashi da ya arce da wata mota ta naira miliyan 55 a kwanakin baya a Abuja, ya bayyana cewa ba da nufin sata ya dauki motar ba. Ya ce kawai dai ya tafi.
Wani magidanci a birnin tarayya Abuja, Raphael Chima, ya nemi Kotun kwastumare mai zama a birnin tarayya ra raba aurensa da Joy saboda bata kaunar zaman lafiya.
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya gana da tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan da gwamnonin jihohin Imo, Ogun da Kwara a fadarsa Aso Villa da ke Abuja.
Tsohon shugaban ma'aikatan jihar Imo, Uche Nwosu ya shawarci Bola Tinubu akan rabon kudaden tallafi inda ya ce ya kamata kudin su kai N30,000, don isa ga kowa.
Bayan kara tsadar litar man fetur, layin ababen haea ya cika gidajen mai maƙil musamman waɗanda ba su kara farashi ba har kawo yanzu a Kano da birnin Abuja.
Hukumar gidajen yarin Najeriya ta ce akalla fursunoni biyar ne suka kammala digiri a gidan gyaran hali na Kuje da ke birnin Tarayya Abuja yayin zamansu a gidan.
Bincike ya nuna cew an ƙara tashin farashin litar man fetur daga N539 zuwa samanda N600 a birnin tarayya Abuja, an gano cewa farashin ya kai naira 617 yau.
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya aike da saƙon ta'aziyya da jaje ga fitaccen ɗan kasuwa, Mangal bisa rasuwar matarsa da Imam Adigun bisa rasuwar mahaifiyarsa.
Jam'iyyar APC ta sake ɗage babban taron masu ruwa da tsaki da kuma taron majalisar zartarwa ta ƙasa (NEC) har sai baba ta gani bayan samun sauyin shugabanci.
Abuja
Samu kari