Mafi karancin albashi
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya shiga ganawa da wakilan gwamnatin tarayya a tattaunawar da ake yi kan mafi karancin albashin ma'aikatan Najeriya.
Daniel Bwala ya bayyana cewa kamata ya yi gwamnati ta kara tayin da ta yi na za ta rika biyan ma'aikata N60,000a matsayin mafi karancin albashi a Najeriya.
Gwamnatin tarayya ta kara yiwa yan kwadago magana kan yajin aiki da ta shiga, ta ce yajin aikin zai kara jefa talakawa cikin wahalar rayuwa sama da wanda suke ciki.
Kungiyoyin kwadagon Najeriya NLC da TUC sun dakatar da yajin aikin da suka shiga a fadin kasar saboda rashin samun daidaito kan sabon mafi karancin albashi.
Shugabar kungiyar ma'aikatan lafiya ta Najeriya, Bamgbose Betty ta koka kan cewa albashin da ma'aikata ke karba a yanzu ba ya wuce kwana uku ya kare.
Kungiyar kwadago NLC ta fitar da sanarwa da safiyar yau Talata 4 ga watan Yuni kan ci gaba da yajin aiki inda ta ce sai an ji daga gare ta kan matakin da za ta dauka
Kungiyar masu jigilar mahajjata ta kasa AHOUN ta bukaci kungiyoyin NLC da TUC sun dakatar da yajin aiki saboda kaucewa taba addini da jawo wa mahajjata asara.
Rahotanni sun bayyana cewa wakilan gwamnatin tarayya da ƴan kwadago sun kamma zaman da aka kira na gaggawa kan yajin aiki a ofishin SGf George Akume.
Kungiyar ma'aikatan kotu reshen birnin tarayya Abuja sun rufe manyan kotuna tare da hana alkalai, lauyoyi da masu shigar da kara aiki saboda yajin aikin NLC.
Mafi karancin albashi
Samu kari