Peter Obi
Tsohon shugaban tsagerun Neja Delta, Asari Dokubo ya aike da matasa zuwa harabar kotun zaben shugaban ƙasa. Matasan ɗauke da alluna sun je goyon bayan Tinubu.
Yau za a yanke hukuncin shari’ar zaben 2023, Tolu Bankole ya fitar da jawabi a Abuja, ya nuna babu dalilin jin dar-dar, ya na mai ganin nasara ta na hannunsu.
Fasto Eunice wacce ya kafa cocin Covenant Of God, a ranar Talata, 5 ga watan Satumba, ta bayyana cewa ta hango zabin Allah a tsakanin Atiku, Obi da Tinubu.
Duk inda aka san rigima za ta iya barkewa yau a Abuja, an baza ‘yan sanda da dakarun NSCDC. Dama an sanar da cewa za a haska zaman kotun a gidajen talabijin.
Babban malamin cocin nan Fasto Kingleo Elijah ya bayyana cewa ya hasaso wasu daga cikin magoya bayan Atiku Abubakar, Peter Obi da Bola Tinubu na kuka, yayinda.
Jigon jam'iyyar PDP, Cif Olabode George, ya yi tsokaci dangane da batun shari'ar zaɓen da ke shirin gudana tsakanin Atiku, Obi da Tinubu ranar Laraba mai zuwa.
Tun bayan dawowar dimukradiyya a shekarar 1999 ake ta faman shari'a kan zabubbuka a Najeriya don kalubalantar zabe, mafi yawa na kan mulki ne ke cin nasara.
An bukaci ma’aikatan kotun daukaka kara da su zauna a gida a ranar Laraba, 6 ga watan Satumba, wanda aka tsayar don yanke hukuncin a kotun zaben shugaban kasa.
Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa ko kadan bai damu ba ganin yadda ake shirin karkare shari'ar zaben shugaban kasa a ranar Laraba 6 ga watan Satumba a Abuja.
Peter Obi
Samu kari