Bayan Ya Koma Mulki, An Ji Dalilin Gwamna Fubara na Amincewa da Dokar Ta Baci a Ribas
- Gwamna Siminalayi Fubara ya yi jawabi kai tsaye ga al'ummar jihar Ribas bayan komawa bakin aiki yau Juma'a 19 ga Satumba 2025
- Fubara ya jaddada cewa babu kalar sadaukarwar da ba zai iya yi ba wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Ribas
- Ya ce bayan ayyana dokar ta baci a watan Maris, mutane sun rika matsa masa ya kalubalanci matakin amma ya zabi hada kai da Tinubu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Rivers - Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya bayyana dalilin da yasa ya amince da dokar ta baci da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ayyana a watan Maris.
Gwamna Fubara ya ce ya yarda da dokar ne domin bai wa shugaban kasa hadin kai wajen dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Ribas.

Source: Facebook
Tribune Nigeria ta ce Fubara ya bayyana hakan ne a cikin jawabin kai tsaye da ya yi ga al’ummar jihar da misalin karfe 6:00 na yammacin ranar Juma’a.
Me yasa Fubara ya amince da dokar ta-baci?
Gwamna Fubara ya ce watanni shida da jihar ta shafe a ƙarƙashin dokar ta baci lokaci ne mai wahala, amma ya zaɓi yin aiki tare da Shugaban Ƙasa da Majalisar Dokoki ta Ƙasa.
“A matsayina na gwamna, na amince da dokar ta baci kuma na zaɓi haɗa kai da Shugaban Ƙasa da Majalisar Dokoki, saboda zan iya kowace sadaukarwa wajen tabbatar da zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci gaban Ribas.
Fubara ya ƙara da cewa ya shanye duk wata matsin lambar da aka yi domin ya kalubalanci sahihancin dokar ta baci, ciki har da dakatar da tsarin dimokuraɗiyya a Ribas.
Ina makomar rikicin siyasar jihar Ribas?
Ya lura cewa shiga tsakani da Shugaba Tinubu ya yi ne ya taimaka wajen samun sulhu tsakanin manyan ‘yan siyasa a jihar, ciki har da tsohon gwamna Nyesom Wike, ‘yan majalisar jihar da shi kansa.
“Muna da yakinin cewa rikicin siyasa ya zama tarihi, kuma an sake dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Jihar Ribas, duk da cewa mun ɗauki darussa masu muhimmanci daga lokacin dokar ta baci,” in ji Fubara.
Ya yi kira ga shugabannin siyasa da masu ruwa da tsaki a jihar da su manta da duk wani sabani, su kuma haɗa hannu don amfanin al’umma, in ji rahoton Daily Trust.

Source: Facebook
A madadin jihar Ribas, Fubara ya gode wa Shugaba Tinubu bisa “irin kulawarsa ta uba da kuma yadda ya shiga tsakani wajen kawo ƙarshen rikici tare da dawo da cikakken tsarin mulkin dimokuraɗiyya a Jihar Ribas.”
Wannan na zuwa ne bayan Shugaba Tinubu ya ɗage dokar ta baci da ta ɗauki watanni shida a Jihar Ribas, wacce aka ayyana domin magance matsalolin siyasa da na mulki.
Fubara ya mika godiya ga Tinubu da Wike
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya mika godiya ga Shugaban Kasa, Bola Tinubu da Ministan Harkokin Abuja Nyesom Wike.
Fubara, wanda ya koma gidan gwamnatin Ribas a karon farko ya ce Tinubu Wike sun ba da gudummuwa gagara misali wajen dawo da zaman lafiya a jihar.
Mai Girma Gwamnan ya jaddada muhimmancin hadin kai, sulhu da kwanciyar hankali, ya na mai cewa zaman lafiya ya fi zama dan Sarki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


