Ana Shirin Haɗaka don Kayar da Tinubu, Ƴar Majalisar Tarayya Ta Fice daga YPP

Ana Shirin Haɗaka don Kayar da Tinubu, Ƴar Majalisar Tarayya Ta Fice daga YPP

  • Clara Nnabuife, wakiliyar mazabar Orumba ta Arewa/Kudu a majalisar wakilai, ta sauya sheka daga jam’iyyar YPP zuwa APGA
  • Ta ce ta tattauna da ƴan mazabarta kafin ta yanke hukuncin fice wa daga cikin jam'iyyar YPP da su ka zaɓe ta a kai bisa wasu dalilai
  • Daga cikin dalilanta, Hon. Nnabuife ta yi an mayar da ita saniyar ware a tsohuwar jam'iyyarta, saboda haka dole ne ta canza gida
  • A baya-bayan nan dai, ana ta samun ƴan majalisun tarayya su na watsar da jam'iyyarsu, sai dai da yawansu sun koma APC ne

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Clara Nnabuife, wakiliyar mazabar Orumba ta Arewa/Kudu (Anambra) a majalisar wakilai, ta sauya sheka daga jam’iyyar YPP zuwa jam’iyyar APGA.

Kara karanta wannan

Shirin kawar da gwamnatin APC: Sababbin jam'iyyu na tururuwar yin rajista da INEC

Mataimakin kakakin majalisar wakilai, Benjamin Kalu, ne ya karanta wasikar sauya shekar Hon. Nnabuife a zauren majalisar a zaman da aka yi a ranar Alhamis.

Majalisa
Yar majalisa ta sauya sheka Hoto: House of Representatives
Asali: Facebook

The Cable ta ruwaito ƴar majalisar, wacce ta fito daga jihar Anambra ta na zargin an ware ta daga harkokin jam’iyyar YPP, wanda hakan ne ya sa ta yanke shawarar barin jam’iyyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hon. Clara Nnabuife ta kara da cewa ta dauki matakin ne bayan tattaunawa mai zurfi da al’ummar mazabarta kafin ta yanke shawarar sauya shekar.

Ƴar majalisar Orumba ta Arewa/Kudu ta fusata

Jaridar Punch News ta wallafa cewa Nnabuife ta bayyana cewa sabuwar jam’iyyarta za ta ba ta ingantacciyar dama don wakiltar muradun mazabarta.

Ta bayyana cewa:

“Ware ni daga harkokin jam’iyyar YPP da kuma bukatar samun dandali mafi kyau don wakiltar muradin al’ummata shi ne dalilin wannan shawara."

Ben Kalu ya zolayi ƴar majalisar da ta bar YPP

Da yake karanta wasikar sauya shekar, Benjamin Kalu, Wanda ya jagoranci zaman majalisar ma ranar Alhamis ya zolayi Hon. Nnabuife.

Kara karanta wannan

Siyasa kenan: Bayan kare El Rufai a baya, shugabar matan APC ta dawo caccakarsa

Benjamin
Mataimakin shugaban majalisar wakilai, Benjamin Kalu Hoto: Rep Benjamin Okezie Kalu
Asali: Facebook

Cikin raha, ya bayyana cewa da ta sauya sheka ne zuwa jam'iyyarsa ta APC ba APGA ba, da ya ba ta hannu sun yi musabaha saboda murna.

A ‘yan makonnin nan, an samu yawaitar sauya sheka a majalisar wakilai, kuma da yawa daga cikinsu na sauya sheka ne zuwa jam'iyya.mai mulki ta APC.

Yan majalisa na sauya sheka zuwa APC

A ranar 2 ga Oktoba, Chris Nkwonta, wakilin mazabar Ukwa ta Gabas/Ukwa ta Yamma a jihar Abia, ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

A ranar 30 ga Oktoba, Sulaiman Abubakar, wakilin mazabar Gummi/Bukkuyum a jihar Zamfara, ya fice daga PDP zuwa APC.

A ranar 5 ga Disamba, wasu ‘yan majalisar wakilai hudu daga jam’iyyar Labour Party (LP) da wani dan PDP suka sauya sheka zuwa APC. A ranar 11 ga Fabrairu, Amos Magaji daga jihar Kaduna ya bar PDP zuwa APC, sai Kuma ranar 12 ga Fabrairu, Garba Koko daga jihar Kebbi ya sauya sheka daga PDP zuwa APC.

Kara karanta wannan

"Sai mun tashi tsaye," Gwamnan APC ya hango damuwa a zaben 2027

Majalisa ta gaji da ƴan kwangila

A wani labarin, kun ji cewa kwamitin majalisar wakilai ya bayyana damuwa kan yadda aka gudanar da ayyukan gyara a gidajen yari da kaya marasa ingancin da ya dace.

Jagoran kwamitin, Chinedu Oga ya tambayi shugaban gidan gyaran hali yadda ake yin aiki da algus, inda shi kuma ya shaida masa cewa kudin ne ba a sakar masu yadda ya dace ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.