An Yanke Makomar Ganduje, APC Ta Bayyana Yankin da Ta Maida Shugabancin Jam'iyya
- Jam'iyyar APC ta kasa ta amince da maida kujerar shugabancinta zuwa yankin Arewa maso Yammacin Najeriya
- Mai magana da yawun APC, Felix Morka ya bayyana cewa an ɗauki wannan matakin ne a taron kwamitin zartarwa watau NEC karo na 13
- Wannan dai wata dama ce da Ganduje zai ci gaba da zama a kujerar shugaban jam'iyya bayan wa'adin da yake kai a yanzu ya ƙare a 2026
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Kwamitin Zartarwa na Kasa (NEC) na jam’iyyar APC ya kawo ƙarshen taƙaddama kan kujerar shugabancin jam'iyya mai mulki.
Kwamitin NEC ya amince cewa kujerar shugabancin jam’iyya ta kasa za ta ci gaba da zama a yankin Arewa-Maso-Yamma.

Asali: Twitter
Sakataren yada labaran APC, Felix Morka, ne ya bayyana haka bayan taron NEC karo na 13 da aka gudanar a Abuja ranar Laraba, kamar yadda Premium Times ta kawo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
APC ta yanke makomar Abdullahi Ganduje
Ya ce an yanke matakin ne a taron NEC wanda shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da shugaban APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje suka jagoranta.
A watan Agustan 2023, tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ya zama shugaban APC na ƙasa bayan da Abdullahi Adamu ya yi murabus a watan Yuli 2023.
Adamu, wanda ya fito daga jihar Nasarawa a Arewa ta Tsakiya, ya hau mulki a shekarar 2022 kuma ya kamata ya yi aiki har zuwa 2026.
Sai dai murabus dinsa ya ba da damar nada Ganduje, wanda shi kuma dan asalin jihar Kano ne a Arewa-Maso-Yamma.
Ganduje: APC ta kawo ƙarshen ƙorafe-ƙorafe
Wannan mataki na ba Arewa maso Yamma kujerar shugaban APC na ƙasa na iya kawo ƙarshen ƙorafin da ƴan Arewa ta Tsakiya ne yi, waɗanda ke neman a dawo masu da kujerar su ƙarisa wa'adin Abdullahi Adamu.
A tsarin raba mukamai na APC a yanzu, Arewa maso Yamma na da manyan mukamai guda uku: shugaban Majalisar Wakilai, mataimakin shugaban Majalisar Dattawa da shugaban APC.

Asali: Twitter
Babban muƙamin da Arewa ta Tsakiya ta tsira da shi a yanzu shi ne Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), George Akume.
Bola Tinubu ya fito daga Kudu maso Gabas, Kashim Shettima daga Arewa maso Gabas, shugaban Majalisar Dattawa daga Kudu maso Kudu yayin da mataimakin kakakin Majalisar Wakilai ya fito daga Kudu maso Gabas.
Ganduje ya kara samun dama a APC
A halin yanzu dai APC ta amince cewa yankin Arewa maso Yamma ne zai fitar da sabon shugaban jam'iyya na gaba bayan karewar wa'adin shugabannin yanzu.
Ana ganin wannan mataki na iya ƙara karfafa Ganduje a kujerarsa sannan kuma zai taara yadda APC za ta raba muƙamai nan gaba.
Wani matashin ɗan siyasa kuma jigo a APC, Usman Abdullahi ya shaidawa Legit Hausa cewa dama ya yi tunanin haka za ta kasance domin Ganduje yana ƙarfi a siyasar Najeriya.
"Wannan mataki ne mai kyau kuma dama na yi tunanin haka a APC, idan ka duba Ganduje yana da ƙarfi a gwamnatin Tinubu, kuma ya san abin da yake yi.

Kara karanta wannan
A gaban Tinubu da manyan jiga jigai, Ganduje ya bankado abubuwan da ya tarar a APC
"Daga hawansa shugabancin jam'iyya zuwa yau, APC ta samu ci gaba fiye da tunaninka, don haka muna tare da shugabanmu," in ji shi.
Ganduje ya gaji bashin N8.9bn a APC
Kun ji cewa shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya roƙi kwamitin zartarwar jam'iyyar watau NEC ta taimaka wajen warware bashin Naira biliyan 8.9.
Ganduje ya bayyana cewa lokacin da ya karɓi shugabancin APC, ya tarar da bashin nmaƙudan kuɗi da suka shafi harkokin shari'a.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng