Atiku Ya Yi wa Tinubu Kaca Kaca kan Kama Farfesa Yusuf da Sowore

Atiku Ya Yi wa Tinubu Kaca Kaca kan Kama Farfesa Yusuf da Sowore

  • Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya soki gwamnatin Bola Tinubu kan kama Omoyele Sowore da Usman Yusuf
  • Atiku Abubakar ya ce ana amfani da kama ‘yan adawa domin razana su da kuma hana su fadin albarkacin bakinsu
  • Hakan na zuwa ne bayan Atiku ya yi zargin cewa APC na kokarin rusa jam’iyyun adawa domin kafa jam’iyya daya tilo a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi kakkausar suka ga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan kama fitattun ‘yan adawa da ke sukar gwamnati.

Atiku ya ce kama Omoyele Sowore da Farfesa Usman Yusuf da ake zargi da badakalar Naira biliyan 4 wata alama ce ta yadda ake kokarin tauye ‘yancin fadin albarkacin baki a Najeriya.

Kara karanta wannan

Tsohon ɗan Majalisa ya danƙara wa Atiku baƙaken kalamai bayan abin da ya faru a taron BoT

Atiku Tinubu
Atiku ya zargi Tinubu da kama 'yan adawa. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Getty Images

Legit ta tattaro cewa Atiku ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Facebook a ranar Alhamis, 30 ga Janairu, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dama dai Atiku Abubakar ya zargi gwamnatin Bola Tinubu da ruguza 'yan adawa wajen raba makudan kudi.

Atiku: "Za su iya tsare mu baki daya"

Atiku Abubakar ya ce kama Sowore da Farfesa Usman Yusuf wani yunkuri ne na haramta ‘yancin fadin albarkacin baki da kuma hana ‘yan adawa damar bayyana ra’ayoyinsu.

A cewar Atiku Abubakar:

"Lokacin da na bayyana cewa Tinubu da APC na kokarin ruguza jam’iyyun adawa domin kafa jam’iyya daya tilo, wasu sun soki magana ta.
"Amma yanzu ga shi ana ci gaba da kama wadanda suka saba da ra’ayin gwamnati.”

Vanguard ta wallafa cewa tsohon dan takarar shugaban ƙasa a PDP ya kara da cewa idan aka ci gaba da irin haka, to, a ƙarshe, gwamnati za ta iya tsare duk wanda ke sukar ta.

Kara karanta wannan

El Rufa'i ya kara girgiza siyasar Najeriya bayan ganawa da 'yan jam'iyyar SDP a Abuja

Ya ce kama Sowore ba tare da wani kwakwaran dalili ba na daya daga cikin alamun wannan yunkuri, sannan kuma yanzu sun saka Farfesa Usman Yusuf cikin wadanda aka kama.

Su wanene Farfesa Usman da Sowore?

Omoyele Sowore da aka fara kamawa dan gwagwarmaya ne da ya shahara a fadin Najeriya da kasashen waje.

A wata hira da ya yi, Sowore ya ce a lokacin da ya yi gwagwarmaya a 1992 Bola Tinubu yana Sanata ne kuma ya fi shi karfin fada a ji.

A daya bangaren, Farfesa Usman Yusuf ya jagoranci hukumar inshora ta NHIS a lokacin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Farfesa Usman Yusuf ya kasance cikin masu caccakar gwamnatin Bola Tinubu wanda hakan yasa wasu ke ganin kama shi na da alaka da hakan.

Martanin Gumi kan kama Farfesa Yusuf

A wani rahoton, kun ji cewa fitaccen malamin addini a Najeriya, Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya zargi Bola Tinubu da kokarin toshe bakin 'yan adawa a Najeriya.

Kara karanta wannan

A karshe, an samu labarin rashin lafiyar da Tinubu ke fama da ita kafin zama shugaban ƙasa

Sheikh Gumi ya yi maganar ne bayan kama Farfesa Usman Yusuf da ya ce mutum ne mai gaskiya da ya sani kimanin shekaru 49 da suka gabata tun suna jami'a.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng