"Mun Ci Amanar Ƴan Najeriya," Tsohon Minista Ya Bayyana Abin da Ya Faru a Mulkin Buhari

"Mun Ci Amanar Ƴan Najeriya," Tsohon Minista Ya Bayyana Abin da Ya Faru a Mulkin Buhari

  • Tsohon ministan matasa da wasanni, Barista Salomon Dalung ya ce gwamnatin Muhammadu Buhari ta ci amanar ƴan Najeriya
  • Dalung ya bayyana cewa wasu masu karfin faɗa a ji ne suka kewaye Buhari ta yadda bai ma san abin da ke faruwa ba a gwamnatinsa ba
  • Salomon Dalung ya ƙara da cewa gwamnatin da ta shuɗe ba ta tsinanawa ƴan Najeriya komai ba face yaudara da ƙarya har ta sauka

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jos, Plateau - Tsohon ministan matasa da wasanni, Barista Salomon Dalung ya bayyana cewa gwamnatin Muhammadu Buhari ta yaudari ƴan Najeriya.

Dalung, wanda ya riƙe kujerar minista a zangon Buhari na farko, ya amince cewa tsohuwar gwamnatin da ta shuɗe ta ɗauki alkawari kuma ba ta cika ba.

Solomong Dalung da Muhammadu Buhari.
Tsohon ministan Muhammadu Buhari ya amince cewa sun yaudari ƴan Najeriya Hoto: Bar. Solomon Dalung, Muhammadu Buhari
Asali: Twitter

Solomon Dalung ya faɗi haka ne a wata hira da aka yi da shi a gidan rediyon ‘Mic On Podcast’ ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

'Yadda aka yi wa Buhari dabaibayi, aka hana shi sakat a shekaru 8,' Dalung

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Muhammadu Buhari ta ci amana

Tsohon ministan ya nuna rashin jin daɗinsa da abin da gwamnatin Buhari ta yi, ya zarge ta da cin amanar ƴan Najeriya, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Dalung ya ce:

"Na yi takaici matuka saboda abin da muka faɗawa ƴan Najeriya ba shi muka aiwatar ba, mun yi karya kuma mun yaudari al'umma.
"Duk da mun yi amfani da yaudarar da jam'iyyar PDP ta yi wa ƴan Najeriy a yakin neman zaɓe amma sai muka zama kamarsu, mayaudara kuma maƙaryata."

Wasu masu faɗa aji ne suka kewaye Buhari

Dalung ya ƙara da cewa wasu masu ƙarfin faɗa a ji ne suka yi amfani da tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari wajen cimma burinsu.

Ya bayyana cewa sai da Muhammadu Buhari ya zama tamkar bako a gwamnatinsa saboda yadda masu karfin faɗa a ji suka mamaye shi.

Yadda jam'iyyar APC ta karɓi mulki a 2015

Kara karanta wannan

"Ban da karba karba": Shekarau ya fadi hanyar samar da shugaban kasa a 2027

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon shugaban hukumar NHRC ya yi ikirarin cewa da zanga-zanga ta yi amfani har Buhari ya ci zaɓen shugaban ƙasa a 2015.

Chidi Odinkalu ya ce yana mamakin yadda gwamnatin APC mai ce ke neman take haƙƙin jama'a na yin zanga-zanga duk da cewa ta wannan hanya ta karbi mulki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262