"Ina da Burin Inganta Rayuwar Talakawa," Ɗan Takarar Sanata Ya Bar Jam'iyyar Accord
- Tsohon ɗan takarar sanatan jihar Oyo ta Tsakiya, Injiniya Faozey Nurudeen ya fice daga jam'iyyar Accord ranar Alhamis
- A wata sanarwa da ya fitar a Ibadan, babban birnin jihar Oyo, matashin ɗan siyasar ya ce nan ba da jimawa ba zai sanar da jam'iyyarsa ta gaba
- Ya ce ya ɗauki matakin barin Accord ne saboda ya fahimci jam'iyyar siyasa na taka rawa wajen samun nasarar ɗan takara a zaɓe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Oyo - Dan takarar kujerar Sanatan Oyo ta tsakiya a jam’iyyar Accord a zaben 2023, Injiniya Faozey Nurudeen ya fice daga jam’iyyar.
Faozey ya tabbatar da ficewarsa daga jam’iyyar Accord ne a wata sanarwa da ya fitar a Ibadan, babban birnin jihar Oyo ranar Alhamis.
Ɗan takarar sanata ya bar Accord Party
Matashin ɗan siyasar ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba zai sanar da jam'iyyar da ya koma, kamar yadda jaridar Leadership ta tattaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Faozey Nuruddeen ya ce:
"Saboda haka na mika takardar barin Accord Party a hukumance ga shugaban jam'iyyar na gundumar Pakoyi/Idode, karamar hukumar Oyo ta Yamma a jihar Oyo.
"Ina da burin taimakon talaka" - Faozey
Ya ce daya daga cikin kudirorinsa na siyasa shi ne ya inganta rayuwar talakawa ta yadda ba za su taɓa mantawa da shi ba, Daily Post ta rahoto.
Tsohon ɗan takarar sanatan ya ce zai cimma wannan buri ne idan ya haɗu da ƴan siyasa masu tunani da kudiri irin nasa, shiyasa zai canza jam'iyya.
Faozey Nurudeen ya ce:
“A zaben da ya gabata, na tsaya takarar sanata mai wakiltar Oyo ta tsakiya a majalisar dattawa karƙashin inuwar jam'iyyar Accord.
"Bisa iko na Allah, jama'ar mazaɓar Oyo ta Tsakiya sun yi imani zan iya wakiltarsu a majalisa, suka kaɗa mun kuri'unsu amma ba mu yi nasara ba.
"Na fahimci cewa jam'iyyun siyasa na taka muhimmiyar rawa a nasarar ɗan takara, wannan ya sa na ɗauki wannan mataki domin komawa inda zan cika buri na."
LP ta fara shirin ture Tinubu a 2027
A wani labarin, kun ji cewa yan jam'iyyar Labour sun yi wani taro na musamman domin fara shirin kifar da gwamnatin APC a zaɓen shekarar 2027.
Shugaban tattaro jama'a na jam'iyyar LP, Marcel Ngogbehi ya ce ba za su yi kasa a gwiwa ba har sai sun shiga Aso Rock Villa a 2027.
Asali: Legit.ng