PDP Ta Firgita da Hukumar DSS Ta Ƙi Faɗin Dalilin Cafke Ƙusa a Jam'iyya
- PDP ta koka kan yadda DSS ta ƙi bari ta gana da jami'inta da aka cafke a jihar Ondo ba tare da dalili ba
- Rahotanni sun bayyana cewa ana zargin tsohon dan takarar gwamnan Ondo da laifuffukan zabe a jihar
- Sakataren yada labaran PDP na Ondo, Kayode Adebayo ya koka kan rashin ganawa da Oladipupo Adebutu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Ogun - Jam'iyyar adawa ta PDP ta shiga yanayi mara dadi bayan zargin wasu jami'an hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta sako ta a gaba.
PDP reshen jihar Ogun ta yi zargin jami'an da damke tsohon dan takarar gwamnan a jihar, Oladipupo Adebutu.
Jaridar Premium Times ta wallafa cewa DSS ta ki bayyana wurin da aka ajiye jagoran bayan kame shi da jami'an hukumar su ka yi a ranar Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
DSS ta kama babba a jam'iyyar PDP
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa Sakataren yada labarai na PDP reshen Ondo, Kayode Adebayo ya nemi dauki kan damke jigo a jam'iyyar.
A sanarwar da Kayode Adebayo ya fitar, ya bayyana cewa har yanzu jami'an tsaron farin kayan ba su shaida masu dalilin kama Oladipupo Adebutu ba.
Dalilin cafke 'dan takaran PDP a 2023
Wasu majiyoyi sun yi zargin cewa jami'an DSS sun cafke tsohon dan takarar gwamnan PDP a Ondo kan zaben baya bayan nan da ya gudana a Ondo.
Rahotanni sun bayyana cewa ko a baya, hukumomi sun zargi Mista Adebutu da laifuffukan da su ka danganci magudin zaben kananan hukumomi a jihar.
Jam'iyyar PDP ta koka kan kama Adebutu
A baya kun ji cewa PDP a jihar Ogun ta ce an kame tsohon dan takararta, Oladipupo Adebutu bisa zarginsa da aikata laifuffukan da su ka sabawa dokar zabe.
Jim kadan bayan cafke Mista Adebutu ne Sakataren yada labaran jam'iyyarsa, Kayode Adebayo ya ce lauyoyinsa ba su samu damar ganawa da shi ba har safiyar Talata.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng