Sanatan NNPP Ya Samu Saɓani da Kwankwaso, Ya Faɗi Shirinsa a Zaben 2027
- Sanatan Kano ta Kudu, Kawu Sumaila ya ce faɗansa da shugaban NNPP na jihar ba zai shafi siyasarsa a zaɓen 2027 ba
- Kawu ya tabbatar da cewa saɓani ya shiga tsakaninsa da jagoran NNPP, Rabiu Kwankwaso amma ba wai sun rabu ba ne
- Rikici ya ɓarke tsakaninsa da Hashimu Dungurawa bayan ya bukaci gwamnan Kano ya maida hankali wajen yi wa al'umma aiki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila mai wakiltar Kano ta Kudu ya ce al’ummar mazabarsa ne kaɗai za su yanke makomarsa a siyasa.
Kawu Sumaila ya ce dangantakarsa da shugaban NNPP na Kano, Hashim Suleiman Dungurawa, ba ta da alaƙa da batun siyasarsa a zaɓe mai zuwa.
Sanata Kawu ya yi wannan furucin ne a wata hira da jaridar Daily Trust ranar Litinin, 18 ga watan Nuwamba, 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanatan NNPP ya faɗi makomarsa a 2027
Da yake tsokaci kan siyasar 2027 mai zuwa, sanatan ya ce mutanen mazaɓar Kano ta Kudu ne kaɗai ke da alhakin yanke wanda zai wakilce su a majalisar dattawa.
"Abin da mutanena za su duba shi ne wane aiki na yi a shekara hudu, me suka samu daga tarayya, ba za su tsaya ɓata lokaci kan alaƙata da shugaban jam'iyya ba," in ji Kawu.
Kawu Sumaila, wanda a yanzu haka yake shari'a da Dungurawa, ya musanta zargin cin amanar jam'iyyar NNPP.
Sanata Kawu ya tabbatar da saɓani da Kwankwaso
Sai dai ya tabbatar da cewa ya samu saɓani da jagoran NNPP na ƙasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, kamar yadda Punch ta kawo.
Kawu Sumaila ya ce:
"Ba wai mun raba gari ba ne, mun samu saɓanin ra'ayi game da wasu abubuwa, ina nan daram a NNPP, sannan kotu ce za ta warware saɓani na da shugaban jam'iyya."
Rikicin ya samo asali ne tun lokacin da Kawu Sumaila ya shawarci Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya maida hankali kan yiwa Kano aiki maimakon biyayya ga Kwankwaso.
Barau na shirin karbe Kano a 2027
A wani rahoton, an ji cewa Sanata Barau I. Jibirin ya ce tururuwar da ƴaƴan NNPP ke yi zuwa APC alama ce ta abin da zai faru a Kano a zaɓen 2027.
Mataimakin shugaban majalisar dattawan ya ce babu sauran ɓurɓushin NNPP ta mazaɓarsa watau jihar Kano ta Arewa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng