Dan Takarar Gwamna Ya Tashi da Kuri'u 1,162, Ya Fadi Wanda Ya Jawo Ya Fadi Zaben Ondo

Dan Takarar Gwamna Ya Tashi da Kuri'u 1,162, Ya Fadi Wanda Ya Jawo Ya Fadi Zaben Ondo

  • Dan takarar gwamna a zaben Ondo da ya kammala, Ayodele Olorunfemi ya fadi wanda ya jawo masa matsala
  • Ya zargi jagora kuma tsohon dan takarar shugaban kasa a jam'iyyarsa, Peter Obi da wasu da jawo masa nakasu
  • Olorunfemi shi ne ya zo na biyar a zaben gwamnan Ondo da kuri'u 1,162 yayin da APC ta yi nasara da kuri'u 366,781

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Ondo - Ayodele Olorunfemi, dan takarar gwamnan jihar Ondo a zaben da aka kammala a karshen mako ya fadi wanda ya jawo masa matsala.

Gwamna mai ci a jihar, Lucky Aiyedatiwa ne ya yi nasara a zaben da kuri’a 366,781, Agboola Ajayi na PDP ya take masa baya da kuri’a 117,845.

Kara karanta wannan

Yadda APC ta sha ruwan kuri'u, Aiyedatiwa ya koma kujerar gwamnan Ondo

Zaben
Dan takarar gwamna a Ondo ya zargi Peter Obi ya jawo masa faduwa a zaben Hoto: Peter Obi/Nigeria Labour Congress HQ
Asali: Facebook

Jaridar The Cable ta wallafa cewa Ayodele Olorunfemi da jam'iyyar LP sun zo na biyar a zaben gwamnan da kuri’a 1,162.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Olorunfemi ya fadi dalilin faduwarsa zaben Ondo

Jaridar Punch ta wallafa cewa dan takarar gwamnan Ondo a inuwar LP, Ayodele Olorunfemi ya fadi wadanda ya ke zargi da tade shi a zaben.

Ya dora alhakin kayen da ya sha a kan kungiyar kwadago ta kasa (NLC) da tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi.

“Yadda na fadi zaben gwamnan Ondo:” 'Dan takara

Ayodele Olorunfemi ya ce kafewa da Peter Obi da NLC su ka yi na tsayar da Olusola Ebiseni a matsayin dan takara ne ya kawo cikas.

A jaji-birin zaben gwamnan Ondo ne Olorunfemi ya yi nasara a kotu na mayar da sunansa a matsayin mai yi wa LP takara a zaben gwamnan.

APC ta yi nasara a zaben jihar Ondo

A baya kun ji cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta bayyana gwamnan Ondo, Lucky Aiyedatiwa da komawa kan kujerarsa bayan ya doke jam'iyyu 18 da ke neman kujerar.

Kara karanta wannan

An kammala zaben Ondo, INEC ta fadi wanda ya yi nasara, an jero kuri'un APC, PDP

A ranar Asabar, 16 Nuwamba, 2024 ne mazauna jihar su ka kada kuri’arsu a zaben da APC su ke kan gaba, inda daga karshe APC mai mulki ta yi rinjaye, jam'iyyar adawa ta PDP ta zo na biyu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.