Yadda APC Ta Sha Ruwan Kuri'u, Aiyedatiwa Ya Koma Kujerar Gwamnan Ondo
Jam'iyya mai mulki ta APC ta sake samun nasara a zaben gwamna a Najeriya, inda dan takararta, Lukcy Aiyedatiwa ya koma kujerar da ya ke kai ta gwamnan jihar Ondo.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Ondo - Jama'ar Ondo sun mayar da gwamna Lucky Aiyedatiwa kujerar gwamnan jihar a zaben da ya gudana ranar Asabar 16 Nuwamba, 2024.
Kamar yadda shugaban APC na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya rika ikirari, jam'iyyar ta yi nasara a zaben da ya karawa APC karfi a Najeriya.
Legit ta tattaro yawan kuri'un da APC ta samu, hadi da na babbar jam'iyyar adawa na PDP a zaben da ya gabata a wannan rahoto;
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Yawan kuri'un da APC ta samu a zaben Ondo
Jaridar This day ta ruwaito cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta ba APC nasara a dukkanin kananan hukumomi 18 na jihar Ondo.
Babban jami'in tattara sakamakon zaben, Farfesa Olayemi Akinwunmi ya jero sakamakon da APC ta samu a kananan hukumomin;
1. Akure ta Arewa - 14, 451
2. Okitipupa 26, 811
3. Akoko ta Arewa maso Gabas - 25, 657
4. Akure ta Kudu - 32, 969
5. Ose - 16, 555
6. Akoko ta Arewa maso Yamma - 25, 010
7. Akoko ta Kudu maso Gabas - 12, 140
8. Ondo ta Yamma - 20, 755
9. Owo - 31, 914
10. Akoko ta Kudu maso Yamma - 29, 700
11. Irele - 17, 117
12. Ifedore - 14, 157
13. Ondo ta Gabas East - 8, 163
14. Ile Oluji/Oke-Igbo - 16, 600
15. ldanre - 9, 114
16. Karamar hukumar Ilaje - 24,474
17. Karamar hukumar Ese Odo - 14511
18. Karamar hukumar Odigbo - 26683
Yadda PDP ta fadi zaben jihar Ondo
Farfesa Olayemi Akinwunmi ya bayyana cewa jam'iyyar PDP ce wacce ta zo ta biyu a zaben da ta rika ikirarin za ta samu nasara, kamar yadda Vanguard ta wallafa.
Farfesa Akinwunmi ya jero sakamakon da PDP ta samu a zaben, inda tsohon mataimakin gwamna, Agboola Ajayi ya sha kasa;
1. Akure ta Arewa - 5, 787
2. Okitipupa - PDP 10, 233
3. Akoko ta Arewa maso Gabas 5, 072
4. Akure ta Kudu - 17, 926
5. 0se - 4, 472
6. Akoko ta Arewa maso Yamma -5, 502
7. Akoko ta Kudu maso Gabas - 2, 692
8. Ondo ta Yamma - 6, 387
9. Owo - 4, 740
10. Akoko ta Kudu maso Yamma - 5, 517
11. Irele - 6, 601
12. Ifedore - 5, 897
13. Ondo ta Gabas - 2, 843
14. Ile Oluji/Oke-Igbo - 4, 442
15. Idanre - 8, 940
16. Karamar hukumar Ilaje - 3623
17. Karamar hukumar Ese Odo - 7814
18. Karamar hukumar Odigbo - 9348
Tinubu ya magantu kan zaben Ondo
A baya mun ruwaito cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya ba yan adawa shawara su garzaya kotu matukar su na da korafi kan yadda hukumar zabe ta INEC ta gudanar da aikinta.
A gefe guda kuma, shugaban ya yaba da yadda INEC ta bayyana APC matsayin wacce ta yi nasara da kuri'u 366,781 bayan doke takwararta, PDP da kuri'a 117, 845 a zaben Asabar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng