'Ku wuce kotu': Tinubu Ya Magantu bayan Zaben Ondo, Ya ba Jam'iyyun Adawa Shawara
- Shugaban kasa, Bola Tinubu ya taya Gwamna Lucky Aiyedatiwa murnar lashe zaben gwamnan jihar Ondo da aka yi a jiya Asabar
- Shugaban ya kuma yabawa hukumar zabe ta INEC kan gudanar da zaben cikin lumana da kuma adalci ba tare da matsaloli ba
- Tinubu ya shawarci sauran jam'iyyu da ba su gamsu da sakamakon ba da su dauki matakin shari'a domin neman hakkinsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya yi magana bayan sanar da sakamakon zaben jihar Ondo a yau Lahadi 17 ga watan Nuwambar 2024.
Tinubu ya taya Gwamna Lucky Aiyedatiwa murnar lashe zaben da aka gudanar a jiya Asabar 16 ga watan Nuwambar 2024.
Tinubu ya yabawa hukumar INEC a Ondo
Shugaban ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da hadiminsa, Dada Olusegun ya wallafa a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya yabawa hukumar INEC bisa gudanar da zaben cikin adalci da kuma lumana ba tare da samun matsala ba.
Sai dai kuma Tinubu ya bukaci wadanda ba su gamsu da sakamakon ba da su je kotu kamar yadda tsarin doka ya tanadar.
Ondo: Tinubu ya yabawa sauran jam'iyyu 17
Shugaban kasar musamman ya kira sauran jam'iyyu 17 da suka fafata a zaɓen inda ya yaba musu bisa halayen dattaku da suka nuna yayin gudanar da zaben.
Tinubu ya ce an samu nasarar hakan ne bisa wayewa da kuma sanin ya kamata da yan jihar Ondo ke nunawa.
Daga bisani, Tinubu bai manta da jami'an tsaro ba musamman yan sanda da NSCDC da NYSC da FRSC da sauran wadanda suka ba da gudunmawa a zaben.
Ganduje ya magantu bayan nasara a Ondo
Kun ji cewa shugaban jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya, Abdullahi Ganduje ya taya Gwamna Lucky Aiyedatiwa murnar lashe zaben Ondo.
Ganduje ya yabawa Shugaba Bola Tinubu kan irin gudunmawa da goyon baya da yake ba jam'iyyar APC wurin ganin ta samu nasarori.
Wannan na zuwa ne bayan hukumar INEC ta sanar da Gwamna Aiyedatiwa na jam'iyyar APC wanda ya lashe zaben da aka gudanar.
Asali: Legit.ng