Ondo : Dan Takarar PDP Ya ga Ta Kansa, Ya Fadi Kulle Kullen da APC Ta Shirya
- Jam'iyyar PDP ta fara korafi kan zaben da ake cigaba da tattarawa a jihar Ondo inda ta zargi hukumar INEC da rashin shiri
- Dan takarar PDP, Ajayi Agboola ya nuna damuwa kan yadda aka yi ta samun korafe-korafe a zaben da aka gudanar
- Wannan na zuwa ne yayin da Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jam'iyyar APC ke kan gaba a zaben inda ya lashe kananan hukumomi 15 daga 18
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Ondo - Yayin da ake cigaba da tattara sakamakon zaben jihar Ondo, jam'iyyar PDP ta kadu da halin da ake ciki.
Dan takarar gwamna a PDP, Ajayi Alfred Agboola ya yi fatali da yadda ake hukumar INEC ke tafiyar da lamarin.
PDP ta fara zargin rashin tsari a zabe
The Nation ta ce Agboola ya tabbatar da kulle-kulle da APC ta yi yayin da aka sanar da kananan hukumomi 15.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Agboola ya soki yadda hukumar INEC ta gudanar da zaben inda ya ce an samu korafe-korafe da dama kan zaben.
Ya koka kan yadda hukumar INEC ta gaza gudanar da zabe mai inganci a jiha guda daya kacal wanda ke nuna akwai matsala a Najeriya.
Dan takarar PDP ya fadi matsalar INEC
"Tsarin ba shi da kyau ko kadan kuma an samu korafe-korafe da dama a wurare daban-daban kan yadda ake tafiyar da zaben."
"Idan har hukumar INEC ba za ta iya gudanar da zabe mai inganci ba a jiha daya, ya zama dole mu gane cewa mun fara gangarawa cikin matsala."
"Ina tunanin da gangan hakan ya faru daga hukumar INEC da kuma kwamishinan zabe da aka turo jihar Ondo."
Ajayi Agboola
Aiyedatiwa ya lashe kananan hukumomi 15
Kun ji cewa jam'iyyar APC ta yiwa babbar abokiyar hamayyarta, watau PDP dakan sakwara a zaben gwamnan jihar Ondo na ranar Asabar.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana sakamakon kananan hukumomi 15 yayin da ake jiran isowar sauran uku.
Sai dai daga iya kananan hukumomi 15 da aka bayyana, APC ta lashe dukkaninsu ba tare da PDP ta samu nasara ko a guda daya ba.
Asali: Legit.ng