Zaben Ondo: Abin da APC da PDP Suka Samu a Kananan Hukumomi 15
- Jam'iyyar APC mai mulki jihar Ondo ta ba PDP tazara mai nisa a sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi 15 da aka sanar
- Ɗan takarar APC, Lucky Aiyedatiwa ya ba takwaransa na PDP, Agboola Alfred Ajayi tazara mai nisa a sakamakon zaɓen da INEC ta sanar
- Ana jiran sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi uku kafin hukumar zaɓe ta INEC ta sanar da wanda ya samu nasarar lashe zaɓen
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Akure, jihar Ondo - Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta sanar da sakamakon zaɓen gwamnan Ondo na ƙananan hukumomi 15.
Hukumar INEC ta kuma sanar da tafiya hutun tattara sakamakon zaɓen, inda za a ci gaba a ranar Lahadi 17 ga watan Nuwamba da misalin ƙarfe 12:00 na rana.
APC ta ba PDP rata a zaɓen gwamnan Ondo
Jaridar Tribune ta ce a sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi 15 da aka bayyana, jam'iyyar APC mai mulki ke kan gaba, sai kuma jam'iyyar PDP ke biye da ita a baya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƙananan hukumomi 15 da aka riga aka bayyana sun haɗa da Okitipupa, Akure ta Arewa, Ifedore, Ondo ta Yamma, Ileoluji Oke-Igbo, Idanre, da Irele.
Sauran sune Akoko ta Kudu maso Yamma, Owo, Ondo ta Yamma, Akoko ta Kudu maso Gabas, Akoko ta Arewa maso Yamma, Ose, Akoko ta Arewa maso Gabas, Akure ta Kudu maso Yamma.
Sauran ƙananan hukumomi uku da ake dakon samun sakamakonsu sun haɗa da Ese Odo, Ilaje da Odigbo.
Yayin da jam’iyyar APC da ɗan takararta, Lucky Aiyedatiwa, suka samu jimillar ƙuri’u 268,144, ɗan takarar PDP, Agboola Ajayi, ya samu kuri’u 79,125.
Jam'iyyar APC na kan gaba a dukkanin ƙananan kananan hukumomi 15 da aka bayyana sakamakonsu.
Sai dai sakamakon zaɓen sauran ƙananan hukumomin uku zai taka rawar gani wajen samun wanda zai lashe zaɓen.
Jam’iyyar PDP za ta yi fatan ganin ta kulle tazarar da APC ta ba ta, har ma ta wuce ta a sauran ƙananan hukumomin da suka rage.
Mataimakin Aiyedatiwa ya yi abin kirki
A wani labarin kuma, kun ji cewa ɗan takarar mataimakin gwamna na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaɓen gwamnan jihar Ondo, Olayide Adelami, ya yi abin arziƙi a rumfar zaɓensa.
Olayide Adelami, ya samu nasarar lashe zaɓe a rumfar zaɓensa a zaɓen gwamnan jihar da ake gudanarwa na ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamban 2024.
Asali: Legit.ng