Zaben Ondo 2024: Aiyedatiwa Ya Sake Bayar da Tazara ga Dan Takarar PDP

Zaben Ondo 2024: Aiyedatiwa Ya Sake Bayar da Tazara ga Dan Takarar PDP

  • Hukumar zaɓe ta INEC ta sanar da sakamakon zaɓen gwamnan jihar Ondo na ƙananan hukumomi 15
  • Ɗan takarar gwamna na jam'iyyar APC, Lucky Aiyedatiwa ya lashe dukkanin ƙananan hukumomin inda ya ba takwaransa na PDP tazara mai yawa
  • Hukumar INEC ta kuma ɗage ci gaba da tattara sakamakon zaɓen har zuwa ƙarfe 12:00 na rana a ranar Lahaɗi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, nishaɗantarwa da nishaɗi

Jihar Ondo - Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta ƙara sanar da sakamakon zaɓen gwamnan Ondo na ƙananan hukumomi biyu waɗanda APC ta lashe.

Hukumar INEC ta sanar da sakamakon zaɓen ƙananan hukumomin Okitipupa da Akure ta Arewa bayan ta dawo daga dogon hutu.

Aiyedatiwa ya ba da rata a zaben Ondo
Aiyedatiwa ya ba Agboola tazara a zaben gwamnan Ondo Hoto: Agboola Alfred Ajayi, Hon. Lucky Orimisan Aiyedatiwa
Asali: Twitter

Aiyedatiwa ya lashe ƙananan hukumomi 15

Jaridar Tribune ta rahoto cewa ɗan takarar gwamnan APC, Lucky Aiyedatiwa, ya lashe zaɓen a ƙananan hukumomin biyu da aka sanar.

Kara karanta wannan

Zaben Ondo: Abin da APC da PDP suka samu a kananan hukumomi 15

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lucky Aiyedatiwa ya ƙara ba abokin hamayyarsa na jam'iyyar PDP, Agboola Alfred Ajayi, tazara a zaɓen.

Tun da farko Aiyedatiwa ya lashe dukkkanin ƙananan hukumomi 13 da hukumar INEC ta sanar da sakamakonsu inda ya ba da tazarar sama da ƙuri'u 178,000.

Yanzu da aka sanar da sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi 15, Aiyedatiwa ya samu ƙuri'u 301,113 yayin da Ajayi ya samu ƙuri'u 97,051 ya zuwa yanzu.

Idan aka koma batun ba da tazara, Aiyedatiwa yana kan gaba da ratar ƙuri'u 204,062.

INEC ta ɗage tattara sakamako

Yayin da ake dakon sakamakon zaɓe daga ragowar ƙananan hukumomi uku, hukumar INEC ta ɗage tattara sakamakon zaɓen zuwa ƙarfe 12:00 na ranar Lahadi.

Baturen zaɓen wanda shi ne shugaban jami'ar gwamnatin tarayya da ke Lokoja, Farfesa Olayemi Akinwunmi, ya ce an ɗage tattara sakamakon zaɓen saboda nisan da ragowar ƙananan hukumomin uku suke da shi.

Aiyedatiwa ya lashe rumfar zaɓensa

Kara karanta wannan

Hukumar INEC ta ɗaura kaso 98% na sakamakon zaben gwamnan jihar Ondo a IReV

A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jam'iyyar APC ya samu nasarar lashe sakamakon zabe a rumfar da ya ƙaɗa kuri'a a jihar Ondo.

Gwamna Aiyedatiwa, wanda ke fafutukar ci gaba da mulki, ya kaɗa kuri'a ne a rumfar zaɓe mai lamba 5, Ugbo Ward 4, Obenla da ke karamar hukumar Ilaje.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng