Zaben Ondo 2024: Dan Takarar Gwamna Ya Fadi Rawar da Tinubu Zai Taka
- Ɗan takarar gwamnan jihar Ondo na jam'iyyar Zenith Labour Party (ZLP), Dr. Abass Mimiko ya yi magana kan zaɓen
- Abass Mimiko ya bayyana cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ba zai tsoma baki ba a zaɓen gwamnan na ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamban 2024
- Ɗan takarar na ZLP ya kuma yabawa hukumar INEC da jami'an tsaro kan yadda zaɓen na gwamnan ke gudana a jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Ondo - Ɗan takarar gwamna na jam’iyyar Zenith Labour Patry (ZLP) a Ondo, Dr. Abass Mimiko, ya yi magana kan rawar da Shugaba Bola Tinubu zai taka a zaɓen gwamnan jihar.
Abass Mimiko ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa Shugaba Bola Tinubu ba zai tsoma baki a zaɓen gwamnan da ke gudana a jihar ba.
Abass Mimiko wanda ƙanin tsohon Gwamna Olusegun Mimiko ne ya bayyana hakan ne bayan kaɗa ƙuri’arsa a Yaba, da ke a ƙaramar hukumar Ondo ta Yamma, cewar rahoton jaridar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me ɗan takarar ZLP ya ce kan Tinubu
"Ina da cikakken ƙwarin gwiwa cewa Shugaba Bola Tinubu ba zai nuna ɓangaranci ba. Zai kasance mai adalci kuma ɗan ba ruwanmu, ba tare da la'akari da jam'iyyarsa ba."
"Don haka ya ragewa ƴan jihar Ondo su yanke shawarar cewa suna son shugabanci nagari."
"A koda yaushe ina cewa mutanen da ke mulkin mu ba sa aiwatar da manufofi masu kyau da shugaban ƙasa yake da su."
"An ninka kuɗin da ake ba jihohi duk wata amma babu abin kirki na ci gaba da aka yi da su."
- Dr. Abass Mimiko
Ɗan takarar na ZLP, wanda ya yabawa INEC da hukumomin tsaro bisa yadda suka gudanar da zaɓen, ya bayyana fatansa na cewa jam'iyyarsa za ta samu nasara.
Mataimakin ɗan takarar PDP ya hango matsala
A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin ɗan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a Ondo, Mista Festus Akingbaso, ya nuna damuwa kan zaɓen gwamnan jihar.
Mista Festus Akingbaso ya nuna damuwa ne game da ƙwararar ƴan daba a ƙaramar hukumar Idanre a yayin zaɓen gwamnan da ake gudanarwa a jihar.
Asali: Legit.ng