Ondo: ‘Abin da Zai Saka ni Karbar Kaddara Idan Na Fadi Zabe’: Dan Takarar APC
- Dan takarar gwamna a jam'iyyar APC a Ondo, Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya yi magana kan zaben da ke gudana a jihar
- Gwamna Aiyedatiwa ya yaba da yadda tsarin zaben ke gudana cikin lumana inda ya ce akwai hasashen APC za ta lashe zabe
- Sai dai gwamnan ya ce idan har aka yi zaben cikin gaskiya da adalci zai karbi dukan sakamakon da aka bayyana ko da bai yi nasara ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Ondo - Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jihar Ondo ya yi magana kan zaben da ake gudanarwa a yau Addabar 16 ga watan Nuwambar 2024.
Gwamna Aiyedatiwa ya fadi dalili daya da zai sanya shi karbar ƙaddara idan ya fadi zabe a jihar bayan kammala tattara sakamako.
Dan takarar APC ya yi magana kan zabe
Aiyedatiwa ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo da Channels TV ta wallafa a yau Asabar 16 ga watan Nuwambar 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Aiyedatiwa ya ce idan har aka yi zaben cikin gaskiya da adalci ko da kuwa bai yi nasara ba zai karbi ƙaddara cikin sauki.
Gwamnan ya ce tabbas zaben na tafiya yadda ake so kuma dukan alamu sun nuna APC ce za ta yi nasara.
Aiyedatiwa ya fadi sharadin yarda da sakamakon zabe
"Idan har aka sanar da sakamakon zabe kuma APC ba ta yi nasara ba, za mu karbi ƙaddara amma ba sai dai idan babu korafe-korafen almundahana da magudin zaɓe."
"Amma idan aka samu matsaloli kan zaɓen, abin da mutum zai yi shi ne zuwa kotu domin neman hakkinsa."
- Gwamna Lucky Aiyedatiwa
An yi harbe-harbe yayin zaben jihar Ondo
Kun ji cewa an shiga fargaba bayan wasu miyagu sun yi ta harbe-harbe a kauyen Ofosun da ke jihar Ondo da safiyar yau Asabar.
Rahotannin sun tabbatar da cewa harbe-harben ya tilasta mazauna yankin shigewa gidajensu saboda fargaba.
Wannan na zuwa ne yayin da ake cigaba da kada kuri'a a zaben gwamna da ake yi a yau Asabar 16 ga watan Nuwambar 2024.
Asali: Legit.ng