Bidiyo: Yadda Dan Takarar SDP a Zaben Gwamnan Ondo, Olorunfemi Ya Kada Kuri'arsa
- Dan takarar gwamnan jihar Ondo karkashin jam'iyyar LP, Festus Ayo Olorunfemi ya kada kuri’arsa a yau Asabar
- An rahoto cewa Olorunfemi ya kada kuri’ar ne a mazabarsa Ajowa-Akoko, karamar hukumar Akoko ta Arewa maso Yamma
- Olorunfemi ya samu shiga cikin zaben ne a ranar Juma'a bayan kotu ta ba INEC umarnin maye sunansa da na Olusola Ebiseni
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ondo - Dan takarar gwamna na jam’iyyar Labour Party (LP) a zaben Ondo Festus Ayo Olorunfemi ya kada kuri’a a zaben jihar da ke gudana.
A yau Asabar, 16 ga watan Nuwamba ne hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta ke gudanar da zaben gwamnan jihar na Ondo.
Ondo 2024: Dan takarar LP ya kada kur'a
Rahoton Channels TV ya nuna cewa Olorunfemi ya kada kuri’arsa a mazabarsa da ke Unit 8, Ward 5, Ajowa-Akoko, karamar hukumar Akoko ta Arewa maso Yamma.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A ranar Juma’ar da ta gabata ne INEC ta sanya sunansa a zaben gwamnan jihar bayan wani hukuncin da kotu ta yanke na hana takarar Olusola Ebiseni.
Kotun daukaka kara ce ta soke hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke wanda ya umarci INEC ta amince da Olusola Ebiseni a matsayin dan takarar jam’iyyar LP.
Bidiyon kada kuri'ar dan takarar LP
A sanarwar da INEC ta fitar a shafinta na X, ta ce za ta bi umarnin kotun tare da sanya sunan Festus Ayo Olorunfemi a matsayin sahihin dan takarar LP a zaben.
Kalli yadda ya kada kuri'a a kasa:
Duba wasu labarai kan zaben Ondo
'Abin da zai faru idan na fadi zben gwamnan Ondo,' dan takarar SDP ya magantu
Kai tsaye: Yadda zaben gwamnan jihar Ondo ke gudana, PDP, APC sun ja daga
Ondo 2024: Jami'an hukumar DSS sun cafke wani da jakunkunan kudi wajen zabe
Ondo: Dan takarar PDP ya hango matsala
A wani labarin, mun ruwaito cewa dan takarar jam’iyyar PDP a zaben gwamnan Ondo, Agboola Ajayi, ya kada kuri’arsa a gundumar Apoi,karamar hukumar Ese-Odo.
Agboola Ajayi ya zargi hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da nuna son kai, yana cewa an samu jinkirin fara zabe a sassa da dama na jihar.
Asali: Legit.ng