Zaben Gwamnan Ondo: An Cafke Mai Sayen Kuri'u Dauke da Tulin Kudi a Jakunkuna
- Wani bidiyo da ke yawo ya nuna lokacin da jami'an DSS suka cafke wani da ake zargin mai sayen kuri'u ne a zaben Ondo
- Rahoto ya nuna cewa an cafke mutumin ne a gunduma ta 4, rumfar zabe ta 007, da ke wajen makarantar St. Stephen, Akure
- A cikin bidiyon, an ga mutumin ya fito da jakunkuna biyu da ake zargin suna shake da tsabar kudi da nufin sayen kuri'u
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Ondo - A wani gagarumin yunkuri na dakile magudin zabe, jami’an hukumar DSS sun cafke wani da ake zargin mai sayen kuri’u ne a zaben gwamnan Ondo da ke gudana.
An kama wanda ake zargin dauke da wasu jakunkuna biyu, wadanda ake kyautata zaton suna makare da kudi domin sayen kuri'un mutane a rumfunan zabe.
Ondo: DSS ta cafke mai sayen kuri'u
Kamen dai ya faru ne a gunduma ta 4, rumfar zabe ta 007, dake wajen makarantar firamaen St. Stephen da ke Akure a Jihar Ondo, a cewar rahoton Channels TV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da kama wannan kamen, hukumar DSS ta aike da sako mai karfi cewa ba za ta amince da sayen kuri’u da sauran nau’ukan cin hanci da rashawa na zabe ba.
An zuba ido sosai a zaben gwamnan Ondo, inda masu ruwa da tsaki daban-daban suka yi kira da a gudanar da sahihin zabe kuma cikin lumana.
Bidiyon yadda aka cafke mai sayen kuri'un
A cikin bidiyon da gidan talabijin din ya wallafa, an ga lokacin da jami'an DSS suka tsayar da mutumin a cikin motarsa, inda suka tirsasa shi ya bude bayan motarsa.
Da farko dai mutumin ya so ya yi gardama, amma da ya fahimci babu wasa a cikin lamuran jami'an tsaron ya sa ya bude bayan motar inda aka ga jakunkuna biyu.
Jami'an tsaron sun tursasa shi fito da jakunkuna tare da wata adda, inda suka sanya shi cikin wata babbar mota kirar 'Coasta', yayin da jama'a suka fara dandazo a wajen.
Kalli bidiyon a kasa:
Asali: Legit.ng