Zaɓen 2024: Muhimman Abubuwa 7 da Ya Kamata Ku Sani Game da Jihar Ondo
Ondo - Jihar Ondo da aka kirkiro a shekarar 1976 tana daga cikin cibiyoyin noma a Najeriya kuma Allah ya albarkace ta da ma'adanai daban-daban.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamba, 2024, hukumar zaɓe watau INEC ta tsara gudanar da zaɓen gwamna a jihar da ke Kudu maso Yammacin Najeriya.
Yayin da shirye-shiryen zaɓen gwamna suka yi nisa, yana da kyau kusan wasu abubuwa masu muhimmanci game da jihar Ondo.
Legit Hausa ta duba wasu muhimman abubuwa guda bakwai game da Ondo wadanda suka bayyana dimbin tarihinta, tattalin arziki, da al'adun gargajiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Tarihin kafa jihar Ondo
A bayanan Wikipedia, an kirkiro jihar Ondo ne a ranar 3 ga watan Fabrairu, 1976 daga tsohon lardin Ondo na jihar Yamma a Najeriya.
Jihar ta haɗa iyaka da jihohin Kwara da Kogi daga Arewa, Edo daga Gabas, Delta a Kudu maso Gabas, Osun da Ogun daga Yamma, da kuma tekun Atlanta daga Kudu.
2. Faɗin ƙasar Ondo da muhalli
Ondo tana da faɗin ƙasa (15,500 km²) da sanannun wurare kamar dajin Mangrove Swamp da ke kusa da Benin, dazuka masu zafi, gandun daji da ke tsaunun Yoruba a Arewacin jihar.
Waɗannan wurare da faɗin ƙasa na matukar taimakawa mazauna a ɓangarori daban-daban kamar noma.
3. Cibiyar noma
Noma shi ne kashin bayan tattalin arzikin jihar Ondo, ita ce jihar da ke sahun gaba a samar da koko a Najeriya.
Bayan Koko, manoma a Ondo suna noman abubuwa da dama da suka haɗa da auduga, taba, katako, shinkafa, dawa, masara, rogo, kayan lambu, da 'ya'yan itatuwa.
Haka nan kuma ana yin sana'o'in gargajiya irinsu ƙera tukwane, saƙar tufafi, ɗinki, kafinta, da ƙira da sauran ayyuka makamantansu.
4. Ma'danan da Allah ya ba Ondo
Allah ya albarkaci jihar Ondo da ma'adai da suka haɗa da man fetur, kwal, yumɓu bakin ƙarfe, sinadarin Pyrites da sauransu, cewar rahoton da Africa Check ta wallafa.
Wadannan albarkatun suna taka rawa wajen bunkasa harkokin masana'antu da ci gaban tattalin arziki.
5. Ci gaban biranen Ondo
Akure, babban birnin jihar Ondo ya samu ci gaba matuka, inda za iya cewa ya zama cibiyar kasuwanci da masana'antu.
Birnin na kunshe da Jami'ar Fasaha ta Tarayya da wuraren buɗe ido da suka shahara kamar ruwan Ikogosi da tsaunin Idanre.
6. Tsarin siyasa
Jihar Ondo dai tana tafiya ne a karkashin tsarin mulkin dimokuradiyya, wanda ya kunshi gwamna da majalisar dokoki.
Kamar yadda dokar ƙasa ta tanada, tsarin zaɓe zagaye biyu ne, na farko kafin ɗan takara ya samu nasara yana bukatar samun kaso 25% na kuri'un da aka kaɗa kashi biyu cikin uku na ƙananan hukumomin Ondo.
7 Al'adu da addinai mabanbanta a Ondo
Yarbawa ne suka mamaye mafi yawan birane a Ondo kamar Idanre, Akoko, Akure, Ikale, Ilaje, Ondo, Ese Odo, da kuma Owo, amma akwai ƴan ƙabilar Ijaw a Kudu maso Gabashin jihar.
A ɓangaren addini kuma galibin mazauna Ondo na bin addinin Kiristanci ne, inda ‘yan tsiraru ke bin addinin Musulunci da kuma addinin Yarabawa na gargajiya.
Al'adun gargajiya, karfin tattalin arziki da muhimman wuraren da ke Ondo ya sa ta yi fice a fagen siyasa da harkokin tattalin arziki a Najeriya.
Matakan kaɗa kuri'a a zaben Ondo
A wani rahoton, an ji cewa hukumar zaɓe INEC ta gama shirin gudanar da zaɓen gwamna a jihar Ondo ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamba.
To sai dai duk da kowane ɗan kasa na da haƙƙin kaɗa kuri'a, akwai abubuwan da ake bukata gabanin a ba ka dama ka zaɓi wanda kake so.
Asali: Legit.ng