Dalla Dalla: Abubuwan da Mutum ke Bukata Kafin Kaɗa Kuri'a a Zaben Gwamnan Ondo
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ondo - A ranar Asabar mai zuwa, 16 ga watan Nuwamba, 2024 za a gudanar da zaɓen gwamnan jihar Ondo da ke shiyyar Kudu maso Yammacin Najeriya.
Wannan zaɓe na zuwa ne makonni bakwai bayan kammala zaɓen gwamnan jihar Edo wanda jam'iyyar APC ta samu galaba.
Hukumar zaɓe ta kasa mai zaman kanta watau INEC ita ke da alhakin shiryawa da ɗaukar nauyin wannan zaɓe da za a yi jibi asabar.
To sai dai duk da kowane ɗan kasa na da haƙƙin kaɗa kuri'a, akwai abubuwan da ake bukata daga kowane mutum gabanin a ba shi damar dangwalawa wanda yake so.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sakamakon haka Legit Hausa tattaro maku wasu muhimman abubuwan da ‘yan jihar Ondo ke bukata kafin su sauke nauyin da ke kansu na zaɓe.
Abubuwan da ake bukata domin kaɗa kuri'a
Hukumar zaɓe INEC ta wallafa matakan da ya kamata mutum ya bi kafin a ba shi damar kaɗa kuri'a a kowane irin zaɓe.
Duk da INEC ta fitar da wannan matakai ne a lokacin babban zaɓen 2023 amma har yanzu zai yi amfani ga mazaunan jihar Ondo a zaben da ake shirin yi nan da ƴan kwanaki.
1. Shekaru 18 ko sama da haka
Dole ne duk wanda zai kaɗa kuri'a a kowane irin zaɓe ba wai na Ondo kaɗai ba, sai ya cika shekaru 18 ko kuma sama da haka.
A dokar zaɓen Najeriya, wanda bai kai shekara 18 ba, ba zai samu damar kaɗa kuri'a ba.
2. Mallakar katin zaɓe (PVC)
Waɗanda suka yi rajista kuma suka mallaki katin zaɓe na dindindin daga hukumar INEC watau PVC ne kaɗai za su kaɗa kuri'a a rumfunan zaɓensu.
Haka nan kuma ko da kana da katin PVC, sai ka tsallake tantancewar na'urar BVAS ta hanyar shacin yatsa ko hoto. A doka, duk wanda bai da PVC ba zai yi zaɓe ba.
3. Gabatar da kai a rumfar zaɓe
Ko da ka na da katin zaɓe, dole ne ka tashi ka kai kanka rumfar zaben da ka yi rijista da ita, ka bi layi sannan ka jefa kuri'a.
Duk wanda bai je rumfar zabensa ba, ya rasa damar wannan zaɓe saboda a dokar Najeriya ba a kaɗa kuri'a ta intanet kuma ba za a biyo ka har gida ba.
Ta ya za ka gano rumfar zaɓenka?
Akwai hanyoyi guda biyu da masu kada kuri'a za su iya tabbatar da rumfar zabensu, ko dai ta hanyar tes ko kuma ta shafin yanar gizon hukumar INEC.
Domin dubawa ta saƙon salula, ana bukatar mutum ya aika sakon sunan jiharsa, sunan ƙarshe da lambobi shida na ƙarshe na jikin katin PVC (VIN) zuwa ɗaya daga cikin lambobin nan: 09062830860, 09062830861.
Yaushe ne lokacin farawa da gama zaɓe?
Za a bude rumfar zabe da karfe 8:30 na safe kuma za a rufe da karfe 2:30 na rana ko kuma lokacin da mutum na karshe a layi ya kada kuri’a ko da 2:30 na rana ba ta cika ba.
Ma'ana dai duk wanda ke kan layi kafin ƙarfe 2:30 na rana za a ba shi dama ya dangwalawa wanda yake so, amma duk wanda ya zo bayan haka ya rasa.
Gwamnatin Ondo ta bada hutun zaɓe
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Ondo na ci gaba da shirye-shiryen tunkarar zaɓen gwamnan da ke tafe a ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamban 2024.
Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya ayyana ranar Juma'a, 15 ga watan Nuwamban 2024 a matsayin ranar hutu ga ma'aikatan gwamnatin jihar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng