Kwankwaso Ya Ba Mutane Mamaki, Ya Faɗi Abin da Ya Fi So a Ayyukan da Ya Yi a Kano

Kwankwaso Ya Ba Mutane Mamaki, Ya Faɗi Abin da Ya Fi So a Ayyukan da Ya Yi a Kano

  • Tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso ya ce gudummawar da ya bayar a ɓangaren ilimi na gina jami'o'i biyu na faranta masa rai
  • Jagoran NNPP ya bayyana cewa a dukkan ayyukan da ya yi lokacin yana matsayin gwamnan Kano, ya fi jin daɗin gina jami'o'in nan
  • Kwankwaso dai shi ne ya gina tubanin Jami'ar Maitama Sule da Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Ɗangote da ke Wudil a lokacin mulkinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso ya ce yana alfahari da jami'o'i biyu da ya kafa a lokacin da yake kan kujerar gwamnan Kano.

Kwankwaso dai shi ne ya assasa jami'ar kimiyya da fasaha da ke Wudil da a yanzu ta koma Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Ɗangote.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna a Arewa ya feɗe gaskiya kan rigimar shugabancin PDP na ƙasa

Rabiu Musa Kwankwaso.
Kwankwaso ya ce gudummuwar da ya bada a ɓangaren ilimi na faranta masa rai a Kano Hoto: Rabiu Musa Kwankwso
Asali: Facebook

Haka nan kuma jagoran NNPP shi ne ya kafa Jami'ar Northawest wadda aka canzawa suna zuwa Maitama Sule University duk a Kano, Punch ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwankwaso ya tuna ayyuka da ya yi a Kano

Sanata Kwankwaso ya bayyana cewa ya fi jin daɗin gudummuwar da ya bayar a ɓangaren ilimi fiye da sauran ayyukan da ya yi a lokacin da yake mulkin Kano.

Tsohon gwamnan ya faɗi haka ne a wurin bikin kaddamar da babban ɗakin taro na zamani wanda aka raɗawa sunan Kwankwaso a Jami'ar Skyline.

"Gudummawar da na bayar a harkar ilimi ne abin da ya fi faranta mani rai,"

- Rabiu Kwankwaso.

Buɗe dakin taron na ɗaya daga cikin ayyukan da aka shirya domin murnar cikar jagoran Kwankwasiyya shekaru 68 a duniya.

"Ina farin ciki da bunƙasa ilimi" - Kwankwaso

Kara karanta wannan

"Mu haɗa ƙarfi da ƙarfe," Gwamna ya faɗi hanya 1 da za a yi maganin ƴan bindiga

Da yake jawabi a wurin taron, Kwankwaso ya ce:

"Ayyukan da na yi irinsu gadojin sama, tituna da bunƙasa harkar noma ba su nake kallo a matsayin gudummuwar da na bayar lokacin ina matsayin gwamna ba.
"Abubuwan da nake jin daɗi kuma nake kallo a matsayin gudummuwata su ne Jami'ar Maitama Sule.da Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Ɗangote da ke Wudil.
"Don haka ina ƙara tabbatarwa mutanen Kano ɗa Najeriya baki ɗaya cewa zan ci gaba da ba da gudummuwa iya karfin a ɓangaren ilimi domin inganta rayuwar al'umma"

Kwankwaso ya kuma yabawa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa jajircewarsa da riko da akidar Kwankasiyya na bunƙasa ilimi da ci gaban al'umma.

Kwankwaso ya ba gwamnati kyautar makaranta

A wani labarin kuma jagoran jam'iyyar NNPP na kasa, Rabiu Musa Kwankwaso ya ba da kyautar sabuwar makaranta ga gwamnatin Kano.

An rahoto cewa Sanata Kwankwaso ya gina makaranta mai ajujuwa tara a garin Rikadawa, karamar hukumar Madobi da ke jihar Kano.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262