APC Ta Kara Kinkimo Rigima a Jihar Kano Ana Shirin Zaɓen Kananan Hukumomi

APC Ta Kara Kinkimo Rigima a Jihar Kano Ana Shirin Zaɓen Kananan Hukumomi

  • Babbar kotun tarayya mai zama a Kano ta sanar da ranar fara sauraron sabuwar ƙarar da APC ta shigar domin hana zaɓen kananan hukumomi
  • APC dai ta roƙi kotu ta hana INEC ba hukumar zaɓen Kano rijistar masu kaɗa kuri'a sannan ta hana shirya zaɓen ranar 26 ga watan Oktoba
  • Jam'iyyun adawa a Kano dai sun nuna damuwa kan kudin da hukumar zaɓe KANSIEC ta zuga na fom ɗin takarar ciyaman da na kansila

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Jam'iyyar adawa a Kano watau APC ta sake garzayawa kotu da nufin hana gudanar da zaɓen kananan hukumomi a jihar.

Babbar kotun tarayya mai zama a Kano ta sanya ranar 11 ga watan Oktoba, 2024 domin fara sauraron karar da APC ta shigar da hukumar zaɓen jihar KANSIEC.

Kara karanta wannan

AKISIEC: Yan daba sun tafka ta'asa, sun bankawa ofishin hukumar zaɓe wuta

Taswirar Kano.
Zaben Kano: Kotu za ta fara sauraron ƙarar APC ranar 11 ga watan Oktoba Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Meyasa APC ta kara shigar da ƙara?

APC ta roki kotun ta hana hukumar zaɓe ta ƙasa INEC bada kundin bayanan masu kaɗa kuri'a domin gudanar da zaɓen kananan hukumomi 44 a Kano, Leadership ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masu ƙara, APC da shugaban jam'iyyar na Kano, Abdullahi Abbas ta hannun lauyansu, Isma'il Abdulaziz sun nemi kotu ta haramta shirya zaɓen ranar 26 ga Oktoba.

Waɗanda ake tuhuma a wannan ƙara sun haɗa da Antoni-Janar na Kano, hukumar KANSIEC, INEC, Antoni-Janar na ƙasa da shugaban hukumar zaɓen Kano.

Kotu ta sa ranar fara zaman shari'a

Mai shari'a Simon Amobeda ya ɗage zaman shari'ar zuwa ranar 11 ga watan Oktoba, 2024, kamar yadda Vanguard ta tattaro.

Da yake hira da manema labarai kan karar, lauyan APC ya ce suna buƙatar kotu ta musu ƙarin haske kan nauyin da doka ta ɗorawa hukumar KANSIEC.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun ɗauki matakin juyawa gwamna baya a gobe zaɓen ƙananan hukumomi

Isma'il Abdulaziz ya ce suna tantamar ko hukumar zaɓen Kano ta rikiɗa ta zama mai tara haraji ne shiyasa ta zabga kuɗin fam N9m na ciyaman da N4m na kansila.

Barau ya ƙara takaita NNPP

Kuna da labarin cewa mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin ya karɓi wasu kusoshi da ƴan NNPP da sauka sauya sheka zuwa APC a Kano.

Barau ya ce ƴaƴan NNPP na ci gaba da tururuwa zuwa APC saboda ayyukan da gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ke yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262