Baki har Kunne: Shugaban APC, Ganduje Ya Samu Manyan Nasarori a cikin Mako 1

Baki har Kunne: Shugaban APC, Ganduje Ya Samu Manyan Nasarori a cikin Mako 1

Shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ya tsallake rijiya da baya bayan kotu ta yi fatali da shari'ar da ke neman a tsige shi daga mukamin shugaban jam'iyya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Makon da ya gabata ya yi wa shugaban APC na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje dadi biyo bayan manyan nasarori biyu da ya samu.

Wannan ta sa Dr. Ganduje ya sha alwashi kan zaben Anambra da Ondo da ke tafe, lamarin da ka iya tabbatar masa da kujerar shugaban jam'iyyar da wasu ke adawa da shi a kai.

Ganduje
Shugaban APC, Abdullahi Ganduje ya samu nasarori cikin mako 1 Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR
Asali: Facebook

Legit ta hado wasu daga cikin nasarorin da Ganduje ya samu a makon da ya wuce;

Kara karanta wannan

'Dan PDP ya fashe da kuka a bidiyo yayin hira a gidan talabijin kan zabe

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Zaben Edo: Ganduje ya jagoranci nasarar APC

Zaben gwamnan jihar Edo ya ja hankalin sosai, musamman ganin cewa PDP ce ta yi mulkin jihar na tsawon shekaru kusan hudu, inda wasu ke zargin an yi amfani da karfin gwamnatin tarayya wajen kwace mulkin ga APC.

Ana ganin dabarun yakin neman zabe da sauran dabarun iya tafiyar da siyasar Ganduje sun taka rawa a nasarar da aka samu, inda Sanata Monday Okpebholo ya yi nasara.

2. Ganduje ya yi nasara a kotu

Bayan shafe tsawon lokaci ana fafatawa a kotu, daga karshe an yanke hukunci kan bukatar sallamar Abdullahi Umar Ganduje daga kujerar shugaban jam'iyya.

Mai shari'a Inyang Ekwo na babbar kotun tarayya ne ya yi watsi da karar da kungiyar APC reshen Arewa ta Tsakiya ta shigar gabanta.

Barista Abubakar Aliyu, lauya ne mai zaman kansa a Kano, ya shaidawa majiyar Legit cewa kotu na da hurumin korar duk karar da ta ga an shigar gabanta ba bisa ka'ida ba.

Kara karanta wannan

Abubuwa 5 da suka jawo APC ta yi nasara a zaben gwamnan Edo

Ya kara da cewa a tsarin tafiyar da jam'iyyu, kowace na da matakan warware rigingimu na cikin gida.

Burin Ganduje kan APC a gaba

Bayan nasarorin da APC ta samu karakashin jagorancin Abdullahi Umar Ganduje, yanzu haka shugaban jam'iyyar ya fara kokarin daukar wasu matakai.

Dr. Ganduje ya bayyana cewa za su yi amfani da dabarun da ya kai su ga nasara a Edo a sauran jihohi da za a yi zabe nan gaba; Ondo da Anambra.

Ganduje, APC sun yi rashin dan jam'iyya

A baya kun ji cewa tsohon dan majalisar dokokin jihar Edo, Honarabul Emmanuel ya sauya tattara kayansa zuwa jam'iyyar PDP bayan ya kammala shawarwari da masu ruwa da tsaki.

Honarabul Emmanuel Agbaje ya dauki matakin koma wa jam'iyyar PDP ne kwanaki kadan bayan ya sanar da ficewa daga APC biyo bayan wasu dalilai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.