2027: Kiran Kwankwaso, Atiku da Obi Su Tararwa Tinubu Ya Fusata Jam'iyyar APC

2027: Kiran Kwankwaso, Atiku da Obi Su Tararwa Tinubu Ya Fusata Jam'iyyar APC

  • APC mai mulki ta mayar da zazzafan martani ga Salihu Lukman, tsohon mataiamkin shugaban jam'iyyar na Arewa maso Yamma
  • Mai magana da yawun APC, Felix Morka ya ce Lukman na ƙoƙarin ɗauke hankalin jama'a daga ayyukan alherin da Bola Tinubu yake yi
  • Wannan dai na zuwa ne bayan tsohon jigon APC ya buƙaci Atiku, Kwankwaso da Obi su haɗa kai domin kayar da Tinubu a 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Jam'iyyar APC ta caccaki tsohon Darakta Janar na ƙungiyar gwamnonin jam'iyyar (PGF), Salihu Lukman.

Jam'iyya mai mulki ta soki Lukman ne bisa kiran da ya yi ga jam'iyyun adawa su haɗa ƙarfi da karfe su kayar da shugaban ƙasa Bola Tinubu a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Tsohon mataimakin shugaban APC ya yi hasashen makomar Shugaba Tinubu a 2027

Salihu Lukman.
Jam'iyyar APC ta caccaki Salihu Lukman kan kiran da ya yi ga ƴan adawa su haɗa maja a 2027 Hoto: Salihu Lukman
Asali: Twitter

Guardian ta tattaro cewa Lukman, tsohon mataimakin shugaban APC na Arewa maso Yamma, ya tattara ya bar jam'iyyar ne saboda walahar da gwamnati ta jefa ƴan Najeriya.

Lukman ya ba Atiku da Kwankwaso shawara

Tun bayan ficewarsa daga APC, Lukman ya fara sukar salon mulkin Shugaba Tinubu wanda a cewarsa ya sauka daga tubalin da aka gina jam'iyya mai mulki a kai.

A makon jiya, ya yi kira ga manyan ƴan takara a 2023, Atiku Abubakar, Rabiu Kwankwaso da Peter Obi su haɗa kai domin kawo karshen mulkin Tinubu a 2027.

2027: APC ta mayar da martani ga Lukman

Da yake martani kan wannan kalamai, sakataren watsa labaran APC, Felix Morka ya ce ɓata lokaci ne kiran PDP da LP su haɗa kai domin rikicin cikin gida kaɗai ya gagare su.

Kara karanta wannan

APC ta kwancewa Tinubu zani a kasuwa kan tsadar rayuwa

Morka ya yi ikirarin cewa Lukman ya yi wannan kira ne domin ɗauke hankalin ƴan Najeriya daga dumɓin ayyukan alheri da gwamnatin Tinubu take yi, rahoton Punch.

A cewarsa, Lukman yana da wata ɓoyayyar manufa ta son zuciya da yake son cimmawa shiyasa ya ɗauki wannan hanyar da ba za ta ɓulle masa ba.

Felix Morka ya kuma soki tsohon jigon APC da cewa ba shi da ƙima da ƙarfin faɗa ajin da zai gayawa ƴan Najeriya wanda za su dangwala wa kuri'unsu da wanda za su juyawa baya.

Da gaske DSS ta kama Peter Obi?

A wani rahoton mai taimakawa Peter Obi kan harkokin yada labarai ya musanta raɗe-raɗin kama tsohon gwamnan kuma jigon LP a gidansa na Anambra.

Val Obienyem ya bayyana rahoton da ke yawo cewa DSS ta kama Obi a matsayin ƙarya mara tushe, ya roki ƴan Najeriya su yi watsi da ita.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262