Nenadi Usman: An Naɗa Mace a Matsayin Shugabar Jam'iyya ta Ƙasa a Najeriya

Nenadi Usman: An Naɗa Mace a Matsayin Shugabar Jam'iyya ta Ƙasa a Najeriya

  • Sanata Nenadi Usman ta zama shugabar kwamitin rikon kwarya na LP ta ƙasa wanda ya ƙunshi mutane kusan 30 daga jihohi
  • Labour Party ta amince da naɗin tsohuwar ministar ne a wurin taron masu ruwa da tsaki wanda ya gudana a gidan gwamnatin Abia
  • Jam'iyyar LP ta kuma naɗa Hon Darlington Nwokocha a matsayin sakataren kwmaitin wanda zai yi aiki tare da Sanata Esher

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abia - Tsohuwar ministar kudi, Sanata Nenadi Usman, ta zama shugabar kwamitin riko na jam’iyyar Labour Party (LP) ta ƙasa mai mambobi 29.

An tattaro cewa an zaɓi Nenadi Usman a matsayin sanata mai wakiltar Kaduna ta Kudu a majalisar dattawa a shekarar 2011 karkashin inuwar jam'iyyar PDP.

Kara karanta wannan

Gwamna ya shiga tsaka mai wuya, jam'iyya ta fara shirin ɗaukar mataki a kansa

Gwamna Otti da Sanata Nenedi Usman.
Nenadi Usman: Tsohuwar minista ta zama shugaban LP ta rikon kwarya Hoto: Ferdinand Ekeoma
Asali: Facebook

Sai dai Sanata Nenadi ta sauya sheƙa daga PDP zuwa Labour Party a kakar zaɓen 2023 da ya gabata, kamar yadda jaridar The Nation ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mace ta zama shugabar jam'iyyar LP

A halin yanzu kuma an zaɓi tsohuwar ministar a matsayin shugabar riko ta jam'iyyar LP.

Ɗaya daga cikin waɗanda aka naɗa a kwamitin rikon kwarya domin su yi aiki da Nenedi Usman shi ne Hon. Darlington Nwokocha, ɗan takarar sanatan Abia ta Tsakiya a 2023.

Labour Party ta ɗauki wannan matakin ne a taron masu ruwa da tsaki wanda ya gudana a babban ɗakin taro na gidan gwamnatin jihar Abia da ke Umuahia yau Laraba.

Ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar LP a zaɓen 2023, Mista Peter Obi ne ya sanar da naɗa kwamitin rikon a wurin taron.

Kara karanta wannan

Mataimakin Shugaban kasa ya shiga taron NEC da manyan attajirai 2, bayanai sun fito

Sanata Esher ta yi jawabin kama aiki

A jawabin kama aiki, tsohuwar ministar kudi ta jaddada bukatar ƴaƴan jam'iyyar su haɗa kai su yi aiki tare, kana ta yi alkawarin yin aiki tukuru domin cimma nasara.

Rahotan Punch ya nuna cewa tsohon shugaban jam’iyyar LP, Julius Abure bai halarci taron ba.

An bukaci Tinubu, Atiku da Obi su haƙura

Kuna da labarin an ba Shugaba Bola Tinubu da Atiku Abubakar da Peter Obi shawara kan sake tsayawa takara a zaben 2027 domin sababbin fuskoki.

Tsohon kakakin kamfen jam'iyyar LP, Kenneth Okonkwo ya ce ya kamata dukansu su janye sake tsayawa takara a zaben sai a samu wasu dabam.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262