Ganduje: Gwamna Ya Ɗauki Zafi kan Masu Sukar Ziyarar da Ya Kai Wa Shugaban APC

Ganduje: Gwamna Ya Ɗauki Zafi kan Masu Sukar Ziyarar da Ya Kai Wa Shugaban APC

  • Gwamnan Nasarawa ya mayar da martani ga masu sukar ziyarar da ya kai hedkwatar APC wajen Abdullahi Ganduje
  • Abdullahi Sule ya ce masu jin haushin wannan ziyara maƙiyan APC ne da ke ƙoƙarin tada masu yamutsi ko ta halin ƙaƙa
  • Gwamnan ya ce ya ziyarci Ganduje ne bayan an gayyace shi domin lalubo hanyar magance rikicin cikin gida da ya addabi APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Nasarawa - Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya ce waɗanda ke sukar ziyarar da ya kai hedkwatar APC ta ƙasa maƙiyan jam'iyyar ne.

Gwamna Sule, wanda shi ne shugaban gwamnonin APC na shiyyar Arewa ta Tsakiya ya zargi masu jin haushin ziyarar da yunƙurin rusa zaman lafiya.

Kara karanta wannan

"Yan bindiga sun shiga uku": Gwamna ya sha alwashi kan matsalar tsaro

Gwamna Abdullahi Sule.
Abdullahi Sule ya caccaki masu adawa da ziyarar da ya kai wa shugaban APC, Dr. Abdullahi Umar Ganduje Hoto: Abdullahi A. Sule
Asali: Facebook

Sule ya ƙara da cewa ba ya kai ziyarar don nuna goyon baya da mubaya'a ga Abdullahi Ganduje a matsayin shugaban APC ba ne, rahoton Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Sule ya caccaki masu sukarsa

Ya ce gwamnoni a matsayinsu na manyan masu ruwa da tsaki na jam’iyyar suna da damar shiga sakatariyar APC ta kasa da haɗuwa da shugabanni a kowane lokaci.

Gwamma Sule ya yi wannan ƙarin haske kan ziyarar ne a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun mai taimaka masa kan harkokin siyasa, Dr Kassim Muh’d Kassim.

Ya ce kuskure ne da yaudarar kai wasu su alaƙanta ziyararsa da goyon bayan Ganduje wanda dama shi ne a kujerar shugaban jam'iyya na ƙasa.

Ganduje yana da abokan hamayya a APC

Wannan bayani na zuwa ne bayan shugaban wata ƙungiyar ƴaƴan APC a Arewa ta Tsakiya, Saleh Zazzaga ya zargi Gwamna Sule da ruguza shirinsu na kwace kujerar Ganduje.

Kara karanta wannan

Gwamnonin PDP sun fusata da kalaman Wike, sun hada shi da jami'an tsaro

Sai dai gwamnan ya ce wadanda ke sukar ziyarar da ya kai makiyan jam’iyyar ne kuma ba su da burin da ya wuce su tada zaune tsaye a APC ko ta halin kaƙa.

Meyasa Gwamna Sule ya je hedkwatar APC?

Gwamna Sule ya ce ya kai ziyarar ne bayan shugabanni sun gayyace shi domin tattauna yadda za a kawo ƙarshen rigingimun cikin gida a jihar Benuwai.

"Abin tambayar shi ne tayaya ziyarar da muka kai sakatariya ta ƙasa ta zama goyon bayan mutumin da tuntuni ya yi ɗare-ɗare a kujerar shugaban jam'iyyar?"

Albashin N70,000: Gwamna Sule ya gana da NLC

A wani rahoton kuma, an ji Gwamna Abdullahi Sule ya bayyana cewa Nasarawa ba za ta iya biyan ma'aikata sabon mafi ƙarancin albashi ba.

Sule ya faɗi haka ne a wurin taronsa da ƴan kwadago kan walwalar ma'aikata wanda ya gudana a gidan gwamnati da ke Lafia.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262