Fadar Shugaban Ƙasa Ta Yi Maganar Man Fetur Ana Tsaka da Wahala a Najeriya

Fadar Shugaban Ƙasa Ta Yi Maganar Man Fetur Ana Tsaka da Wahala a Najeriya

  • Fadar shugaban ƙasa ta sake nanata cewa tallafin fetur ya zama tarihi a Najeriya tun bayan kalaman Bola Tinubu a Mayun 2023
  • Mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga ne ya bayyana haka ranar Talata, 3 ga watan Satumba
  • Onanuga ya musanta rahoton da ake yaɗawa cewa gwamnatin tarayya ta yiwa ƴan Najeriya rufa-rufa wajen biyan tallafin mai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Yayin da ake kukan ƙarin farashin litar man fetur, fadar shugaban ƙasa a Najeriya ta kare Bola Ahmed Tinubu kan batun tallafin man fetur.

Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga ya ce babu abin da Gwamnatin Bola Tinubu ta ɓoye a manufofinta.

Kara karanta wannan

Ganduje: Tinubu, Buhari da wasu ƙusoshin APC za su yanke makomar shugaban APC

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Fadar shugaban ƙasa ta ƙara nanata cire tallafin man fetur tun 29 ga watan Mayu, 2023 Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Onanuga ya bayyana haka ne a shafinsa na X yau Talata yayin da yake martani kan surutun da ake ta yi a Najeriya kan tallafin man fetur.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana zargin Tinubu na biyan tallafin mai

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ka-ce-na-ce da ruɗani kan yadda akw shigo da man fetur da kuma ƙayyade farashi a Najeriya.

Da yake mayar da martani kan rahotannin da ke zargin gwamnati da yaudarar jama'a game da biyan tallafin man fetur, Onanuga ya ce:

"Na karanta jerin labarai da ke caccakar Gwamnatin Tarayya da rashin fadin gaskiya game da biyan tallafin man fetur bayan kamfanin NNPC ya ce yana bin dillalai bashin $6bn."

Gwammatin Tinubu ta nanata matsayarta

Onanuga ya yi fatali da wadannan rahotannin, yana mai cewa marubutan labaran suna tunanin sun fallasa wata rufa-rufar gwamnati ne amma ba su san ba haka abin yake ba.

Kara karanta wannan

Daga karshe an sanya lokacin fara sayar da man fetur na matatar Dangote a kasuwa

"Maganar gaskiya ita ce babu wata rufa-rufa da aka bankaɗo, gwamnatin tarayya ba ta ɓoye komai ba, ta daina biyan tallafin mai tun daga kalaman shugaban ƙasa Bola Tinubu na ranar 29 ga watan Mayu, 2023."
"Tun daga lokacin ba a kara sanya tallafin a kasafin kuɗi ba, babu shi a ƙarin ƙasafin 2023, haka ba a sa shi a kasafin kuɗin 2024 ba," in ji Onanuga.

Man fetur ya haura N1,000 a Kano

A wani rahoton kuma karancin man fetur ya ƙara tsananta yayin da farashin lita ya kai N1,200 a gidajen man ƴan kasuwa a jihar Kano.

Rahotanni sun nuna cewa farashin ya tashi zuwa N904 a gidajen man kamfanin NNPCL, masu ababen hawa sun yi layi suna jira.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262