Hadimin Abdullahi Ganduje Ya Fadi 'Tuggun' da Aka Shiryawa Jam'iyyar APC

Hadimin Abdullahi Ganduje Ya Fadi 'Tuggun' da Aka Shiryawa Jam'iyyar APC

  • Hadimin shugaban APC, Cif Oliver Okpala ya zargi wasu a gefe da yin kokarin jefa jam'iyya mai mulki cikin rudani
  • Okpala wanda shi ne babban mataimaki na musamman ga Abdullahi Ganduje ya ce wasu sun turowa APC yan leken asiri
  • Jawabin Cif Okpala na zuwa bayan kalaman jigo a jam'iyyar, Alhaji Saleh Zazzaga na kin amincewa da shugabancin Ganduje

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja - Babban mai taimakawa shugaban jam'iyyar APC na kasa, Cif Oliver Okpala ya caccaki jigo a jam'iyyar, Alhaji Saleh Zazzaga bayan kalamansa a kan Abdullahi Ganduje.

Cif Okpara ya zargi wasu da kokarin dasa wasu a cikin jam'iyyar domin su haddasa husuma da jawo rarrabuwar kai.

Kara karanta wannan

"Wike ba zai zama mana kadangaren bakin tulu ba," PDP ta fadi dalilin kafa kwamitin ladabtarwa

Ganduje
Hadimin Abdullahi Ganduje ya caccaki masu son kawo rarrabuwar kai a APC Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa daya daga cikin jigo a jam'iyyar, Alhaji Saleh Zazzaga ya nuna kin amincewa da shugaban APC na kasa, Ganduje da wasu kalamai kan gwamna Abdullahi Sule.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Cif Okpala ya bayyana cewa bai kamata Alhaji Zazzaga ya rika kalaman da za su nuna matsalar jam'iyyar a bainar jama'a ba.

"APC ta aminta da Ganduje, Cif Okpala

Jam'iyyar APC ta sake nanata cewa ta aminta da Dr. Abdullahi Umar Ganduje a matsayin shugaban jam'iyyar na kasa, tare da gargadin masu kokarin kawo baraka.

Babban mataimakin shugaban jam'iyyar, Mista Oliver Opkala be ya bayyana haka, inda ya ce bai dace Alhaji Zazzaga ya rika kalaman kokarin kawo rudani ba.

Arewa maso tsakiya sun samu matsayi a APC

Mujahid Zaitawa, jigo a jam'iyyar APC a Kano ya shaidawa Legit cewa bai kamata yan Arewa ta tsakiya su nemi kujerar APC ba.

Kara karanta wannan

Tinubu zai shiga matsala: An gano shirin Atiku, Obi, Kwankwaso na hade kansu a 2027

Zaitawa yana da wannan matsaya ne ganin cewa George Akume daga yanki na Arewa ta tsakiya ne sakataren gwamnatin tarayya.

Jam'iyyar APC ta magantu kan korar Ganduje

A baya mun ruwaito cewa jam'iyyar APC ta musanta labarin da ke yawo na cewa ana shirye-shiryen korar shugaban jam'iyyar, Abdullahi Umar Ganduje daga mukaminsa.

A cewar sanarwar da sakataren jam'iyyar, Sanata Ajibola Basiru ya fitar, ya ce su na da kwarin gwiwa kan yadda Ganduje ke tafiyar da APC, tare da godewa shugaba Bola Tinubu bisa goyon bayansa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.