Atiku Ya Haɗu da Nuhu Ribaɗu da Wani Sanatan APC a Abuja, Hotuna Sun Bayyana
- Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar ya haɗu da Nuhu Ribadu a wurin sallar Jumu'a tare da sauran Musulmi a Abuja
- Atiku dai babban jagoran adawa ne a Najeriya yayin da Nuhu Ribadu ke aiki tare da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a matsayin mai bada shawara kan tsaro
- Bayan Ribaɗu, Wazirin Adamawa ya kuma haɗu da sanata mai wakiltar Bauchi ta Kudu karkashin inuwar APC duk a masallaci jiya Jumu'a, 30 ga watan Agusta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a 2019 da 2023, Alhaji Atiku Abubakar ya haɗu da mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribaɗu.
Manyan jiga-jigan ƴan siyasar biyu sun haɗu kuma sun gaisa a masallacin Jumu'a jiya 30 ga watan Agusta, 2024 a babban birnin tarayya Abuja.
Alhaji Atiku da NSA Nuhu Ribadu duk sun fito ne daga jihar Adamawa da ke shiyyar Arewa maso Gabas a Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Atiku ya gaisa da Sanatan Bauchi
Har ila yau a masallacin Jumu'ar, tsohon mataimakin shugaban kasar ya haɗu da Sanata Umar Buba mai wakiltar Bauchi ta Kudu a majalisar dattawan Najeriya.
Mai taimakawa Atiku kan harkokin yaɗa labarai, AbdulRasheed Shehu ya wallafa hotunan wannan haɗuwa a shafinsa na manhajar X wanda aka fi sani da Twitter.
Hotunan sun nuna yaddda manyan ƴan siyasar suka gaisa da juna cikin farin ciki da girmama juna duk da suna da banbancin jam'iyyun siyasa.
"Atiku Abubakar ya gaisa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu da Sanata Shehu Buba bayan sallar Jumu'a," in shi AɓdulRasheed.
Wannan dai na zuwa ne kusan mako ɗaya bayan manyan ƙusoshin siyasar ƙasar nan sun haɗu a wurin ɗaura auren ɗiyar Atiku a Abuja.
Hotunan haɗuwar Atiku da Ribadu
Atiku ya maida martani ga Bode George
A wani rahoton kuma Atiku Abubakar ya yi wa jigon PDP martani bayan ya ba shi shawarar ya haƙura da yin takara a zaɓen shekarar 2027 mai zuwa.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana cewa halin da gwamnatin Tinubu ta jefa ƴan Najeriya ne a ransa ba tunanin 2027 ba.
Asali: Legit.ng