2027: Ganduje Ya Bayyana Tsare Tsaren da APC Ta Fito da Su a Dukkan Jihohi

2027: Ganduje Ya Bayyana Tsare Tsaren da APC Ta Fito da Su a Dukkan Jihohi

  • Shugaban APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ya fadi wasu tsare tsaren da jami'yya mai mulki ta fito da su a jihohi
  • Abdullahi Umar Ganduje ya ce sun fara shirin tattara cikakkun bayanai kan yadda za su yi rajistar ƴaƴan jam'iyyar ta yanar gizo
  • Haka zalika Abdullahi Ganduje ya bayyana kokarin da yake wajen hada kan ƴaƴan jam'iyyar domin dunkulewa waje ɗaya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ya fadi wasu shirye shiryen da suka fito da su a jam'iyyance.

Abdullahi Ganduje ya ce yanzu haka suna son ganin 'ya'yan jami'yyar sun dunkule waje guda daya daga manya har kanana.

Kara karanta wannan

"Ba mu yi mamaki ba," Jam'iyyar APC ta yi magana kan ficewar babban jigonta

Ganduje
APC ta fitar da tsare tsare a jihohi. Hoto: Abdullahi Umar Ganduje
Asali: UGC

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Ganduje ya koka kan yadda al'amuran siyasa suke tsayawa a jam'iyya sai lokacin siyasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jam'iyyar APC za ta yi rajistar ƴaƴanta

Abdullahi Umar Ganduje ya ce za su yi rajista wa dukkan ƴaƴan APC a kowane mataki da kuma tara bayanansu ta yanar gizo.

Shugaban jam'iyyar ya ce hakan zai taimaka musu wajen tunkarar yakin neman zabe da kuma sanin irin alkawuran da za su yi garesu.

Za a canza fasalin APC a jihohi

Abdullahi Umar Ganduje ya ce sun gaji da ganin yadda ofisoshin jam'iyya ba su aiki a jihohi sai lokacin zabe kawai.

Saboda haka ya ce dole za su canza yadda lamura ke gudana wajen samar da ayyukan da za a rika yi a ofis ofis din jam'iyya a kowane mataki.

Jam'iyyar APC za ta hada kan ƴaƴanta

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta gano matar da ta yi barazanar kashe ƴan Najeriya a Kanada

Punch ta wallafa cewa shugaban jam'iyyar ya bayyana cewa za su samar da tsarin da zai kawo hadin kai a tsakanin dukkan 'yan APC.

Ganduje ya ce dole a samu hadin kai tsakanin masu mulki kamar gwamnoni da sauran masu shugabancin jam'iyyar.

APC ta yi shirin lashe zaben Edo

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa jam'iyyar na shirin ganin jihohin Najeriya 36 sun dawo hannunta.

Ganduje ya nuna ƙwarin gwiwar cewa APC za ta lashe zaɓukan gwamna a jihar Ondo da Edo waɗanda za a yi a wannan shekarar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng