Jerin Abubuwa 2 da Aka Ƙulla da Nufin Wargaza Shirin Tazarcen Bola Tinubu a 2027
- Shugaban kwamitin rikon kwarya na APC a jihar Ribas, Tony Okocha ya yi zargin cewa wasu na yunkurin karɓe jam'iyyar a jihar
- Okocha ya bayyan acewa hakan na ɗaya daga cikin makircin da aka fara kitsawa domin hana Bola Tinubu tazarce a zaɓen 2027
- Jam'iyyar APC mai adawa a jihar Ribs ta kara shiga cikin rigima biyo bayan hukuncin babbar kotun jiha na rusa kwamitin Okocha
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Rivers - shugaban riko na APC a jihar Ribas, Tony Okocha ya ce hukuncin kotu na rusa kwamitin da yake jagoranta wata manaƙisa ce da aka ƙulla da nufin karɓe jam'iyyar.
Mista Okocha ya bayyana cewa rigingimun da suka ɓarke a APC ta jihar Ribas na ɗaya daga cikin abubuwan da aka shirya domin daƙile tazarcen Bola Ahmed Tinubu a 2027.
Rikicin APC: Okocha ya aikawa Tinubu saƙo
Kamar yadda The Nation ta tattaro, shugaban APC na rikon kwarya a Rivers ya ce kotun ba ta da hurumin tsoma baki a harkokin cikin gida na jam'iyyar siyasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sakamakon haka Tony Okocha ya ce ba ruwan kotu da batun shugabancin jam'iyyar.
Da yake jawabi ga ƴan jarida a Abuja, Mista Okocha ya nanata cewa APC ta jima da dakatar da Emeka Bike (wanda ke tutiyar shi ne shugaban APC) da wani Barista Iheanyichukwu Dike.
Tony Okocha ya ce:
"Mu na kotu a matsayinmu na ƴan ƙasa masu bin doka, a wurin mu hukunci ko daga banɗaki ya fito za mu yi biyayya, amma yanzu dai mun shigar da bukatar dakatar da hukuncin a kotun ɗaukaka ƙara.
"Tun da jimawa kotun ƙoli ta raba gardama, ta yanke cewa bai kamata kotuna su riƙa sa baki a harkokin cikin gida na jam'iyyu ba. Zaɓen shugaban jam'iyya lamari ne na cikin gida."
Abubuwa 2 da Okocha ya ambata
1. Hukuncin rusa kwamitin rikon kwarya na APC a Rivers
2. Rigingimun da wasu suka jawo a APC.
Farfesa Falola ya magantu kan zanga-zanga
A wani rahoton kuma Farfesa Toyin Falola na jam'iar Texas ya yi magana kan zanga-zangar nuna adawa da halin ƙuncin da aka yi a ƙasar nan.
Farfesan ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu bai magance matsalolin da suka sanya mutane suka fito kan tituna.
Asali: Legit.ng