Malami Ya Faɗi Wanda Zai Lashe Zaben Shugaban Kasa Idan PDP Ta Fito da Atiku a 2027
- Primate Elijah Babatunde Ayodele ya bayyana cewa jam'iyyar PDP za ta sha kaye matukar ta sake ba Atiku Abubakar tikitin takara a 2027
- A wani faifan bidiyo da ya fitar, babban malamin ya ce Atiku ba zai iya jan ragamar PDP zuwa nasara ba a zaɓen shugaban kasa na gaba
- Wazirin Adamawa ya riƙe kujerar mataimakin shugaban kasa daga 1999 zuwa 2007 kuma ya nemi takara sau da dama bai samu nasara ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Babban limamin cocin evangelical, Primate Elijah Babatunde Ayodele ya yi hasashen cewa PDP ta mutu murus idan ta sake tsaida Atiku Abubakar takara a zaɓen 2027.
Fitaccen limamin kirista ya ce cikin sauƙi APC za ta buga PDP da kasa idan har jam'iyyar adawa ta sake miƙawa Atiku tikitin takarar shugaban ƙasa.
Primate Ayodele ya bayyana haka ne a wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na manhajar X wanda aka fi sani da Twitter ranar Alhamis, 15 ga watan Agusta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tarihin takarar Atiku Abubakar
Legit Hausa ta tattaro cewa Atiku, wazirin Adamawa ya nemi zama shugaban ƙasa sau da dama amma Allah bai ba shi nasara ba.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya nemi ya tsaya takarar kujera lamba ɗaya a Najeriya a 1993, 2007, 2011, 2015, 2019, da kuma 2023.
Ayodele ya yi hasashen takarar Atiku
Limamin cocin ya bayyana cewa idan har Atiku ya lashe tikitin PDP, to jam'iyyar ba za ta kai labari ba.
Ayodele ya ce:
"PDP ku karkaɗe kunnenku da kyau, idan kuna son shan kaye, to ku ba Atiku tikitin takarar shugaban ƙasa, za ku ga yadda za a yi ƙasa-ƙasa da ku, cikin sauki APC za ta samu nasara.
"Atiku ba shi ne mafitar PDP a 2027 ba, idan kuka sake gwada shi, to ku tabbaci haƙiƙa a siyasa PDP ta mutu, ajalin PDP kenan,"
Legas: An maka gwamna a kotu kan rusau
A wani rahoton na daban, an ji wata shugabar makaranta Paulin Eboagwu da mai gidanta sun kai ƙarar gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu a kotu.
Masu karar sun roki babbar kotun jihar Legas ta umarci waɗanda ake tuhuma su biya diyyar N11bn kan rusa ɓangaren makarantarsu ba bisa ƙa'ida ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng