"Akwai Matsala," Malami Ya Hango Abin da Zai Faru a Zaben Shugaban Kasa a 2027

"Akwai Matsala," Malami Ya Hango Abin da Zai Faru a Zaben Shugaban Kasa a 2027

  • Fitaccen malamin kirista, Primate Elijah Babatunde Ayodele ya gargaɗi Bola Tinubu ya tashi tsaye domin daƙile rikicin siyasa
  • Malamin ya yi wannan gargaɗin ne a lokacin da yake hasashen abin da zai iya faruwa a zaben shugaban ƙasa mai zuwa a 2027
  • A wani faifan bidiyo, Ayodele ya ce matukar Tinubu da muƙarrabansa suka gaza yin abin da ya dace, za su fuskanci ƙalubale a zaɓe

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Shugaban wani babban coci a kasar nan, Elijah Babatunde Ayodele ya yi hasashen cewa za a yi, "tashin hankali a siyasa," lokacin babban zaɓen 2027.

Primate Babatunde Ayodele ya roƙi shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya tashi tsaye kuma ya yi abin da ya dace gabanin babban zaɓe na gaba.

Kara karanta wannan

Sace takardun shari'a: Ganduje ya yi wa Gwamna Abba martani mai zafi

Primate Ayodele.
Primate Ayodele ya yi hasashen yadda za ta kaya a zaben shugaban ƙasa na 2027 Hoto: Primate Elijah Babatunde Ayodele
Asali: Facebook

Primate Ayodele ya gargadi Bola Tinubu

Fitaccen malamin addinin kirista ya yi wannan hasashen ne a wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na manhajar X wanda aka fi sani da Twitter.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malamin ya kuma buƙaci shugaban Najeriya da ya yi nazari kuma ya duba yiwuwar sauke farashin man fetur.

Manufofin Tinubu sun fusata ƴan Najeriya

Tun bayan rantsar da shi a watan Mayu, 2023, Tinubu ya ɗauki matakai daban-daban na tattalin araziki, wanda ya hada da cire tallafin man fetur.

Ƴan Najeriya sun yi ƙoƙarin jure waɗannan manufofi na shugaban ƙasa waɗanda suka haifar da wahalhalu da tsadar rayuwa.

Sai dai a cikin watan Agusta da muke ciki, ƴan Najeriya sun fusata sun fito zanga-zanga inda suka nemi a mayar da tallafin man fetur da sauke farashin kayan abinci.

Ayodele ya yi hasashen zaɓen 2027

Kara karanta wannan

Bayan fadin albashin sanatoci, Kawu Sumaila ya yi sabuwar fallasa

Amma da yake bayyana abubuwan da ya hango a zaɓe na gaba, Primate Ayodele ya ce:

"Na hango za a samu tashin hankalin siyasa a 2027. Abin da na ke hangen ya tunkaro mu shi ne idan gwamnatin Tinubu ta gaza lalubo hanyar gyara Najeriya, to akwai matsala."
"Na hango rikici na tunkaro mu, ya kamata Tinubu ya waiwayi kamfanin mai na ƙasa NNPCL domin duba yadda za a sauke farashin man fetur."

2027: Gwamnan Bauchi ya yi maganar takara

A wani rahoton kuma Gwamna Bala Mohammed na Bauchi ya ce Goodluck Jonathan zai iya dawo da Najeriya kan turba mai kyau idan ya koma kan mulki

Da yake martani kan kiraye-kirayen ya fito takara a 2027, gwamnan ya ce ƙofarsa a buɗe take amma ba zai kara da migidansa ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262