Sarki a Arewa Ya Tuɓe Rawanin Sarautar Sanatan APC Saboda Rashin Mutunta Gwamna

Sarki a Arewa Ya Tuɓe Rawanin Sarautar Sanatan APC Saboda Rashin Mutunta Gwamna

  • Mai Martaba Sarkin Bauchi, Dr. Rilwanu Suleiman Adamu ya sauke Sanata Shehu Buba Umar daga sarautar Majidaɗin Bauchi
  • Majalisar masarautar ta ce an ɗauki wannan matakin ne bisa zargin Sanatan da rashin mutunta Gwamna Bala Mohammed
  • Tun farko sanata mai wakiltar Bauchi ta Kudu ya caccaki gwamnan, yana mai zarginsa da karkatar da tallafin shinkafa da taki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bauchi - Masarautar Bauchi ta tuɓe rawanin sarautar gargajiya na ‘Majidadin Bauchi’ daga kan Sanata Shehu Buba Umar.

Masarautar ta ɗauki wannan matakin ne bisa zargin sanatan da rashin mutuntawa da cin mutuncin gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Mohammed.

Gwamna Bala Mohammed.
Sarkin Bauchi ya tsige Sanata Shehu Buba Umar daga sarautar Majidaɗi Hoto: Sen. Bala Mohammed
Asali: Facebook

Sanata Shehu Umar na wakiltar mazabar Bauchi ta kudu a majalisar dattawa ta 10 a karkashin jam’iyyar adawa a jihar watau APC, rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Kotu ta kori korafin yan takarar APC da NNPP, ta fadi wanda ya lashe zaben Sanata

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa marasautar Bauchi ta ɗauki mataki?

Majalisar masarautar ta tabbatar da janye sarauta daga kan sanatan a wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan watan 14 ga Agusta da sa hannun Nasiru Musa a madadin sakataren fada.

Ya ce an amince da janye sarautar daga hannun dan majalisar tarayyar ne a wurin zaman da majalisar masarauta ta yi ranar Laraba ƙaraƙashin Sarkin Bauchi Dr. Rilwanu Suleiman Adamu.

"Majalisar masarauta ta tatauna zargin rashin ɗa'a da ake wa sanatan kuma a karshe ta amince da janye sarautar (Majidaɗin Bauchi) da ta naɗa shi."

Majalisar ta kuma zargi Sanata Buba Umar da rashin mutunta Gwamna Bala da yi masa rashin kunya, matakin da ta ce ya saba da koyarwa da al’adun masarautar Bauchi.

Wane laifi Sanatan Bauchi ta Kudu ya aikata?

A baya-bayan nan, Sanatan Bauchi ta Kudu ya zargi gwamnan Bauchi da karkatar da motocin tallafin shinkafa wanda gwamnatin tarayya ta turo a rabawa talakawa.

Kara karanta wannan

Ana fama da rikicin Kano, gwamnati za ta gurfanar da wani Sarki a gaban kotu

Shehu Buba Umar ya zargi gwamnatin Bauchi da sayar da tallafin kayayyaki kamar Shinkafa da taki wanda Gwamnatin Bola Tinubu ta aiko a rabawa mabukata da nufin rage raɗaɗi.

Da alama wannan ne dai ya sa masarautar Bauchi ta sauke Sanata Buba daga sarautar Majidaɗi.

Gwamna Bala ya faɗi dalilin sukar Tinubu

Kun ji cewa gwamnan jihar Bauchi ya fito ya bayyana dalilinsa na sukar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan halin da ake ciki a ƙasa.

Bala Abdulkadir Mohammed ya ce ya fito ya yi kalamansa ne da zuciya daya domin tunatar da gwamnati kan nauyinta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262