Rigima Ta Ɓarke, Mataimakin Gwamna da Majalisa Ta Tsige Ya Koma Bakin Aiki a Ofis

Rigima Ta Ɓarke, Mataimakin Gwamna da Majalisa Ta Tsige Ya Koma Bakin Aiki a Ofis

  • Rigima ta ƙara ɓallewa tsakanin gwamnatin jihar Edo da Philip Shaibu, mataimakin gwamnan da kotu ta mayar
  • Shaibu ya sanar da cewa ya koma bakin aiki ranar Litinin amma Gwamna Obaseki ya maida martani da cewa sojan gona ne
  • Sai dai Kwamared Shaibu ya jaddada cewa shi ne sahihin mataimakin gwamnan Edo sakamakon hukuncin kotun tarayya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Edo - Mataimakin gwamnan jihar Edo da aka mayar kan mulki, Kwamared Philip Shaibu, ya koma bakin aikinsa ranar Litinin.

Hakan na zuwa ne bayan babbar kotun tarayya ta soke matakin majalisar dokokin jihar Edo na tuge Shaibu, ta umarci ya koma kan muƙaminsa.

Gwamna Obaseki da Philip Shaibu.
Musayar yawu ya barke tsakanin gwamna da mataimakinsa bayan hukuncin kotu Hoto: Governor Godwin Obaseki, Hon. Comrade Philip Shaibu
Asali: Facebook

Shaibu ya koma ofishin mataimakin gwamna

Kara karanta wannan

Sakataren gwamnati ya yi murabus, gwamna ya naɗa wanda zai maye gurbin nan take

A wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na X, Shaibu ya umarci duka hadimansa su dawo bakin aiki ko kuma su fuskanci hukunci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma gargadi bankunan da ke hada-hadar kudaden ofishin mataimakin gwamna ba tare da amincewarsa ba, yana mai bayyana hakan a matsayin haramun.

"Domin biyayya ga kundin tsarin mulkin Najeriya da aka yiwa garambawul, ina mai sanar da komawa bakin aiki a hukumance," in ji Shaibu.

Gwamna Obaseki ya caccaki Shaibu

Jim kadan bayan bayyanar bidiyon, Gwamna Godwin Obaseki, ya maida martani da cewa Shaibu na yiwa mataimakin gwamna sojan gona, don haka a yi watsi da shi.

A wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai na Edo, Chris Nehikhare, ya fitar ya ce:

"Gwamnatin jihar Edo ta samu labarin tsohon mataimakin gwamna, Philip Shaibu yana aika takardu ga ƙungiyoyi da cibiyoyi daban-daban a ciki da wajen jihar, ya na sojan gona.'

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Babban jigo ya faɗi dalili 1 da ya kamata a tsige Tinubu da wasu gwamnoni

"Domin kare waɗannan kungiyoyi muna kara tabbatar da cewa Shaibu ba shi ne mataimakin gwamna ba, duk wata wasiƙa da ya aiko maku ku ɗauke ta a jabu.

Ya ce a halin da ake ciki Omobayo Marvelous Godwins ne mataimakin gwamnan Edo kuma duk wani sako da wani daban zai turo, ciki har da Philip Shaibu jabu ne, rahoton Daily Trust.

Shaibu ya mayarwa gwamna martani

Da yake mayar da martani ga gwamnan ta ofishin yada labaransa, Shaibu ya ce tuni kotu ta ɓinne batun tsige shi daga matsayin mataimakin gwamna.

"A bayyane yake cewa hukuncin kotu ya mayar da Kwamared Shaibu a matsayin mataimakin gwamna kuma dole ne a bi shi.
"A halin yanzu Marvelous Omobayo Godwins shi ne ke yin sojan gona a nan kuma zai iya faɗawa laifin raina kotu. Baya ga haka, hukuncin ya hana hatta gwamna yin katsalandan a aikin mataimakin gwamna."

Obaseki ya naɗa sabon sakataren gwamnati

Kara karanta wannan

"Duk arzikinmu?" Kashim Shettima ya ga rashin dacewar fama da talauci a Arewa

A wani rahoton Godwin Obaseki ya naɗa Joseph Eboigbe a matsayin sabon sakataren gwamnati a jihar Edo bayan Osarodion Ogie ya yi murabus.

Mai magana da yawun gwamnan, Crusoe Osagie ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, 12 ga watan Agusta, 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262