Sakataren Gwamnati Ya Yi Murabus, Gwamna Ya Naɗa Wanda Zai Maye Gurbin Nan Take

Sakataren Gwamnati Ya Yi Murabus, Gwamna Ya Naɗa Wanda Zai Maye Gurbin Nan Take

  • Godwin Obaseki ya naɗa Joseph Eboigbe a matsayin sabon sakataren gwamnati a jihar Edo bayan Osarodion Ogie ya yi murabus daga muƙamin
  • Mai magana da yawun gwamnan, Crusoe Osagie ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, 12 ga watan Agusta, 2024
  • Ogie dai ya yi murabus daga sakataren gwamnatin Edo domin bin umarnin dokar zaɓe a matsayinsa na ɗan takarar mataimakin gwamna a zaɓe mai zuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Edo - Gwamna Godwin Obaseki ya nada Joseph Eboigbe a matsayin sabon sakataren gwamnatin jihar Edo.

Gwamnan ya yi wannan naɗin ne bayan Osarodion Ogie ya yi murabus daga matsayin sakataren gwamnati saboda takarar mataimakin gwamna.

Kara karanta wannan

Mutane sun ƙara samun sauƙi bayan tashin tashinar masu zanga zanga a Arewa

Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo.
Gwamna Obaseki ya nada sabon sakataren gwamnatin jihar Edo Hoto: Godwin Obaseki
Asali: Facebook

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai bai wa gwamna Obaseki shawara ta musamman kan harkokin yada labarai, Crusoe Osagie ya fitar, Channels tv ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna ya naɗa sabon sakataren gwamnati

"Gwamna Godwin Obaseki ya amince da nadin Mista Joseph Eboigbe a matsayin sabon sakataren gwamnatin jihar. Nadin ya fara aiki nan take,” in ji Oasagie.

Eboigbe ya taba zama mai bai gwamna shawara na musamman kan kasafin kudi da tsare-tsaren tattalin arziki sannan kuma ya riƙe kwamishinan kudi. 

Mista Ogie ya yi murabus

Crusoe Osagie ya kara da cewa Gwamna Obaseki ya amince da murabus din tsohon sakataren.

Mista Ogie wanda ya sauka domin cimma burinsa na takarar mataimakin gwamnan jihar Edo a zabe mai zuwa.

A rahoton Tribune Nigeria, kakakin Obaseki ya ƙara da cewa:

Kara karanta wannan

Rigima ta barke, mataimakin gwamna da majalisa ta tsige ya koma bakin aiki a ofis

"Gwamnan ya godewa Ogie bisa jajircewa da biyayyar da ya nuna wajen cika kudirin gina jihar Edo a tsawon shekaru bakwai da suka gabata.
"Obaseki na yi wa Ogie fatan alheri a abin da ya sa a gaba kuma ya yi amanna da cewa zai yi amfani kwarewa da gogewarsa wajen yi wa al’ummar Edo hidima.”

PDP ta caccaki Philip Shaibu

A wani rahoton na daban jam'iyyar PDP a jihar Edo ta yi tofin Allah-wadai kan Philip Shaibu, mataimakin gwamnan jihar Edo da ya koma APC.

Kamar yadda takardar da Debo Ologunagba ya fitar ta bayyana, ra'ayinsa na son kai da zagon ƙasa ga zabin jama'ar Edo ya fito fili.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262