Babbar Kotu Ta Jikawa Ganduje Aiki, Ta Tsige Shugaban APC da Wasu Ƙusoshin Jiha
- Kotu ta sauke muƙaddashin shugaban jam'iyyar APC na jihar Ribas, Cif Tony Okocha, ta dawo da Emeka Beke kan muƙaminsa
- Mai shari'a Sika Aprioku ya ce APC ba ta da hurumin korar zaɓaɓɓun shugabanninta na jiha tare da naɗa kwamitin rikon ƙwarya
- Tuni dai kwamitin riƙon kwaryar APC na jihar Ribas ya yi watsi da wannan hukuncin, ya sha alwashin ɗaukaka ƙara
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Rivers - Babbar kotun jiha mai zama a Fatakwal ta ta soke matakin tsige zaɓaɓɓun shugabannin APC na jihar Ribas karkashin jagorancin Emeka Beke.
Mai shari'a Sika Aprioku na babbar kotun ne ya yanke wannan hukuncin a ranar Litinin, 12 ga watan Agusta, 2024.
Aƙalin ya yanke hukuncin cewa kwamitin ayyuka na jam’iyyar APC ta kasa ya tafka kuskure da ya rusa zaɓaɓɓun shugabanni na jihar Ribas karkashin Emeka haka kurum.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kar yadda jaridar Punch ta tattaro, mai shari’a Aprioku ya bayyana cewa jam’iyyar APC ta ƙasa ba ta da hurumin korar zababbun shugabanni na kowace jiha.
Kotu ta sauke Okocha daga kujerar APC
Haka nan kuma kotu ta ce APC ba ta da ikon naɗa wani kwamitin rikon kwarya gabanin ƙarewar wa'adin zaɓaɓɓun shugabannin jam'iyya.
Sakamakon haka ne kotun ta tsige shugaban APC na rikon ƙwarya na Ribas, Chief Tony Okocha tare da dukkan mambobin kwamitinsa, sannan ta mayar da Emeka.
Mai shari’a Aprioku ya kuma haramtawa Tony Okocha da mambobin CTC ci gaba da ayyana kansu a matsayin shugabannin jam’iyyar APC a jihar Ribas.
Jam'iyyar APC za ta ɗaukaka ƙara
Hukuncin ya biyo bayan karar da Sam Etetegung ya shigar yana ƙalubalantar Abdulahi Ganduje, shugaban APC na kasa da kwamitin CTC.
Kwamitin riko kwarya na APC a jihar karkashin jagorancin Cif Tony Okocha, ya yi watsi da hukuncin da babbar kotun jihar Ribas ta yanke ranar Litinin.
Mai magana da yawun CTC, Chibike Ikenga, ya ce tuni jam'iyyar ta umarci tawagar lauyoyinta su ɗaukaka ƙara zuwa gaba, rahoton Vanguard.
APC ta fara shirin dawo da Ndume
A wani rahoton kuma jam'iyyar APC ta sake magana kan yiwuwar dawo da Sanata Ali Ndume mukaminsa na mai tsawatarwa a majalisa.
APC ta tabbatar da cewa ta fara magana da shugabannin majalisar dattawa kan dawo da Sanata Ali Ndume kan matsayinsa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng