Zanga Zanga: Tsohon Gwamnan Kano Ya Gano Bakin Zaren, Ya Aika Saƙo ga Tinubu

Zanga Zanga: Tsohon Gwamnan Kano Ya Gano Bakin Zaren, Ya Aika Saƙo ga Tinubu

  • Malam Ibrahim Shekarau ya buƙaci gwamnatin Bola Tinubu ta sake nazari kan manufofin tattalin arzikin da ta aiwatar tun bayan hawa mulki
  • Taohon gwamnan Kano ya ce lokaci ya yi da Shugaba Tinubu da hadimansa za su waiwayi baya, su amince da kura-kuransu
  • Wannan kalamai na Shekarau na zuwa ne a lokacin da yan Najeriya ke zanga-zanga kan tsadar rayuwa da yunwa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya ce ya kamata gwamnatin Bola Tinubu ta sake duba manufofinta kuma ta amince da kura-kuranta.

Tattalin arzikin Najeriya ya samu tangarɗa tun bayan cire tallafin man fetur wanda gwamnatin tarayya karkashin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ta yi.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP a Arewa ya shiga matsala kan sukar Tinubu, an gindaya masa sharuda

Malam Shekarau da Bola Tinubu.
Tsohon gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya buƙaci Bola Tinubu ya karbi kuskurensa Hoto: Malam Ibrahim.Sherau, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Haka zalika ƙimar Naira ta faɗi warwas a kasuwar musayar kuɗi duk sakamakon tsare-tsaren gwamnati mai ci, lamarin da ya jawo zanga-zangar matasan Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shekarau ya ba gwamnatin Tinubu shawara

A wata hira da Channels tv cikin shirin siyasa a yau na ranar Jumu'a, Malam Shekarau ya ce lokaci da ya yi da Tinubu da muƙarrabansa za su sake nazari kan tsare-tsaren.

Tsohon gwamnan ya kuma bayyana cewa ya kamata shugaban kasar ya ɗauki kuskurensa idan bukatar hakan ta taso.

Shekarau ya ce:

"Kamar yadda muka sha faɗa a harkar mu ta koyarwa, yana da kyau mu rika ɗaukar darasi daga kura-kuran mu. Ya kamata gwamnati ta zauna ta waiwayi baya.
"Wane wurare ta yi kura-kurai? Wane kuskure ta tafka? Wane furuci ne ta yi a kan kuskure? Wane manufofi ta bullo da su da suka kawo yunwa da hauhawar farashin kayan abinci?

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban ƙasa ya aike da saƙon gaggawa ga Tinubu kan masu zanga zanga

Tun daga furucin Bola Tinubu a ranar rantsar da shi a watan Mayu, 2023, inda ya ce, "tallafi ya tafi," farashin fetur ya nunka sau uku aƙalla yayin da hauhawar farashin kaya ke ƙara tashi.

Ɗaya daga cikin bukatun masu zanga-zangar shi ne a dawo da tallafin man fetur amma Tinubu a jawabinsa ya ce cire tallafi ba gudu ba ja da baya.

Malam Shekarau ya aika saƙo ga Tinubu

Sai dai Malam Shekarau ya ce ya kamata gwamnatin Tinubu ta amince kuma ta ɗauki kura-kuran da ta yi.

"Ku amince akwai wasu kura-kurai da aka tafƙa, mai yiwuwa akwai wasu matakai da aka ɗauka da wasa, yanzu lokaci ne da za a zauna a magance su."

Obasanjo ya aika sako ga Tinubu

A wani rahoton kun ji cewa Cif Olusegun Obasanjo ya gargaɗi gwamnatin tarayya ta biya bukatun matasa masu zanga zanga saboda suna kan gaskiya.

Tsohon shugaban kasar ya ce Najeriya ta samu koma baya bayan ya bar mulki saboda waɗanda suka biyo bayansa ba su yi abin da ya dace ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262