Minista Ya Tona Asirin Gwamnoni, Ya Faɗi Gwamna da ke Sauya Shinkafar Tallafin Tinubu

Minista Ya Tona Asirin Gwamnoni, Ya Faɗi Gwamna da ke Sauya Shinkafar Tallafin Tinubu

  • Ministan raya Neja Delta ya zargi gwamnan jihar Edo da sauya buhunan shinkafar da gwamnatin tarayya ta raba
  • Abubakar Momoh ya ce gwamnoni da dama sun ɓoye buhunan shinkafar da aka ba su domin su rabawa masu karamin ƙarfi
  • Ya ce ya ga bidiyon yadda masu zanga-zanga suka fasa manyan rumbunan ajiya suka wawushe irin waɗannan kayan tallafin

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Edo - Ministan raya Neja-Delta, Abubakar Momoh, ya zargi Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo da sauya buhunan kayan abincin da gwamnatin tarayya ta turo a rabawa talakawa.

Abubakar Momoh ya ce gwamnan yana sauya buhunan ne domin nuna kamar gwamnatinsa ce ta sayo kayan take rabawa mutanen jihar Edo.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: A ƙarshe ƴan Arewa sun jero buƙatunsu, sun aika saƙo ga Shugaba Tinubu

Mamoh da Gwamna Obaseki.
Ministan Tinubu ya zargi Gwamna Obaseki da sauya mazubin shinkafar gwamnatin tarayya Hoto: Abubakar Mamoh, Godwin Obaseki
Asali: Facebook

Ministan ya yi wannan furucin ne a wata hira da Channels tv yayin da yake martani kan zargin gwamnatin tarayya ta gaza cika alƙawarin raba tirlolin abinci 20 a kowace jiha.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan baku manta ba Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya bada umarnin tura tirololin shinkafa 20 ga kowace jiha da Abuja domin karya farashin kayan abinci, Daily Trust ta rahoto.

Minista ya zargi gwamnoni da ɓoye tallafi

Ministan wanda dan asalin jihar Edo ne, ya ce ya kalli bidiyon yadda masu zanga-zanga suka kutsa cikin rumbunan ajiya tare da wawushe buhunan shinkafa da wasu gwamnoni suka ki rabawa talakawa.

Sai dai duk da bai ambaci jihohin da abin ya faru ba, amma a ƴan kwanakin nan masu zanga-zanga sun yi awon gaba da buhunan shinkafa a wani rumbun ajiya a Edo.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta sake magana kan dawo da tallafin man fetur da kawo saukin abinci

Minista ya caccaki Gwamna Obaseki

Abubakar Momoh ya nuna fushinsa kan yadda Gwamna Obaseki, a lokacin da yake jawabi ga masu zanga-zanga, ya faɗa masu cewa zai kai sakonsu ga Shugaba Bola Tinubu.

"Ina ganin duk gwamnan da ya ce bai karbi tirela 20 na shinkafa ba, to bai yi adalci ba.
"Dangane da jihar Edo da ka ambata, ka duba abin da ya faru, mun gani a soshiyal midiya da talabiji yadda mutane ke shiga rumbun adana kayayyaki, suna sace kayan abincin da aka turo."

- Abubakar Momoh.

Gwamnatin Tinubu ya gargaɗi kasashen waje

Kuna da labarin gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ko kaɗan ba za ta lamunce wasu ƙasashen waje su yi mata katsalandan a harkokin cikin gida ba

Ministan harkokin ƙasashen waje wanda ya bayyana hakan ya yi barazanar gwamnatim za ta ɗauki mataki kan duk ƙasar da ta samu da laifi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262