Zanga Zanga Ta Ƙara Ɗaukar Zafi, Matasa Sun Tafka Ɓarna a Hedkwatar Jam'iyyar APC

Zanga Zanga Ta Ƙara Ɗaukar Zafi, Matasa Sun Tafka Ɓarna a Hedkwatar Jam'iyyar APC

  • Masu zanga-zanga sun farmaki hedkwatar jam'iyyar APC reshen jihar Zamfara ranar Litinin, 5 ga watan Agusta, 2024
  • Sakataren yaɗa labarai na APC a jihar, Yusuf Idris ya ce ɓata garin sun lalata muhimman kayayyakin da ke ajiye a ofisoshi
  • Alhaji Yusuf Idris ya buƙaci jami'an tsaro su gaggauta kamo duk masu hannu a harin domin su girbi abin da suka shuka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Zamfara - Wasu ƴan daba daga cikin masu zanga zanga sun farmaki babbar hedkwatar jam'iyyar APC ta jihar Zamfara da ke Arewa maso Yamma ranar Litinin.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ƴan Najeriya galibi matasa ke ci gaba da zanga-zangar nuna adawa da tsare-tsaren gwamnati mai ci da suka kawo wahala.

Kara karanta wannan

Rana ta 5: Zanga zanga ta ɗauki sabon salo, wasu matasa sun yi tsirara a kan titi

Masu zanga zanga.
Masu zanga zanga sun kai hari hedkwatar jam'iyyar APC a Zamfara Hoto: Aliyu Assufy
Asali: Getty Images

APC ta yi tir da farmakin zanga-zanga

Jam’iyyar APC ta reshen Zamfara ta yi Allah-wadai da harin da masu zanga-zangar suka kai sakatariyarta a jihar, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran jam’iyyar APC na jihar, Yusuf Idris ya fitar a Gusau ranar Litinin, 5 ga watan Agusta.

"Jam’iyyar APC reshen Zamfara ta yi Allah-wadai da harin da wasu bata-gari da suka fake a cikin masu zanga zanga suka kai sakatariyar ta.
"Tun ranar Jumu'a da ta gabata APC ta gargaɗi gwamnatin Zamfara kar ta sake ta bari ƴan daba su huce haushinsu a kan jam'iyyar da shugabanninta.
"Kwanan nan ‘yan daba suka farmaki gidan Sanata Sahabi Ya’u (APC, Zamfara ta Arewa) da ke Kaura Namoda, suka yi yunkurin kona gidan tsohon gwamna Bello Matawalle da ke Gusau duk da sunan zanga-zanga."

Kara karanta wannan

Zanga zanga: An kama mutumin da ke ɗinka tutocin ƙasar Rasha a jihar Kano

- Yusuf Idris.

Ya ƙara da cewa jam’iyyar APC ta kuma roki jami’an tsaro da su tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin jama’a a lokacin wannan zanga-zanga, rahoton Punch.

Masu zanga-zanga sun yi wa APC ɓarna

Yusuf ya bayyana cewa duk da haka sai da ƴan daban da sunan zanga-zanga suka farmaki sakatariyar APC da ke kan titin Sokoto da ke cikin garin Gusau ranar Litinin.

Ya ce masu zanga-zangar sun tafka ɓarna, inda suka lalata gilasai, kofofi, tare da kwashe kayayyaki da kayan gini da aka ajiye a cikin ofisoshi.

"Ba za mu lamunci wannan ba kuma muna Allah wadai, muna kira ga jami'an tsaro sun gaggauta kama masu hannu tare da gurfanar da su a gaban ƙuliya."

Ɗan sanda ya harbe matashi a Bauchi

A wani rahoton kuma an shiga yanayin tashin hankali yayin da wani jami'in tsaro ya harbe mai zanga-zanga har lahira a garin Azare da ke jihar Bauchi.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun cafke masu zanga-zangar lumana a Abuja

Wani faifan bidiyo ya nuna yadda wasu mutane suna tarar wa matashin suna dukansa, daga karshe ake zargin cewa jami'in tsaron ya harbe shi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262