Zanga Zanga: Babban Malami Ya Cire Tsoro, Ya Buƙaci Shugaba Tinubu Ya Yi Murabus

Zanga Zanga: Babban Malami Ya Cire Tsoro, Ya Buƙaci Shugaba Tinubu Ya Yi Murabus

  • Wani babban malamin addini ya buƙaci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi murabus idan ba zai iya gyara tattalin arziki ba
  • Farfesa Princewilll Ariwodor ya ce Buhari ya miƙa tattalin arziki mai kyau ga Tinubu amma ya lalata shi da tsare-tsaren da ya zo da su
  • Wannan kira na zuwa ne yayin da ƴan Najeriya suka fara zanga-zanga kan yunwar da manufofin Tinubu suka kawo a ƙasa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abia - Shugaban kungiyar dattawan Abia kuma babban malamin kirista, Archbishop Farfesa Princewill Ariwodor, ya buƙaci shugaban ƙasa ya yi murabus.

Fitaccen malamin ya yi kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya yi murabus idan har ba shi da mafita kan durkushewar tattalin arzikin Najeriya.

Kara karanta wannan

Ana saura kwana 1, gwamnatin Tinubu ta aike da muhimmin saƙo kan zanga zanga

Bola Ahmed Tinubu.
Malamin kirista ya yi kira ga shugaban ƙasa Bola Tinubu ya sauka idan ba zai iya ba Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Malamin ya yi wannan kira ne yayin wata hira da jaridar Vanguard a lokacin da aka fara zanga-zanga kan yunwa da tsadar rayuwa a Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malamin kirista ya aika saƙo ga Tinubu

Ya ce tun farko bai kamata shugaban kasar ya nemi takara ba idan ya san cewa ba shi da mafita ga kalubalen da ke addabar al’umma.

Farfesa Ariwodor ya buƙaci shugaban ya matsa gefe idan ba zai iya share hawayen ƴan ƙasa ba musamman wahalhalun da tsare-tsarensa suka kawo.

Ya bayyana cewa tattalin arziƙin ƙasa ya durkushe, inda ya yi kira ga shugaban ƙasa da sauran muƙarrabansa su ƙara kaimi wajen farfaɗo da shi, rahoton Naija News.

Ariwodor ya buƙaci Bola Tinubu ya sauka

Ariwodor, wanda kwanan nan ya zama shugaban wata kungiyar malaman kiristoci ta duniya ICCOBA a Dublin, ya ce:

Kara karanta wannan

"Ba a Najeriya ƙaɗai ake wahala ba," Fitaccen Sarki ya aika saƙo ga masu shirin zanga zanga

“Ba mu taba fuskantar irin wannan rugujewa a harkokin tattalin arzikin kasar nan ba. Sauran shugabanni za mu iya cewa ta kowane fanni sun fi gwamnatin yanzu.
 "Ya kamata Tinubu ya yi murabus idan ba zai iya gyara tattalin arziki ba, kafin zuwansa ba haka muke rayuwa ba. Buhari ya damka masa mafi kyawun tattalin arziki wanda yanzu ya lalata."

Gwamnatin Jigawa ta rufe mutane a gida

A wani rahoton kuma, Gwamna Umar Namadi ya sanar da sanya dokar hana fita ta tsawon awanni 24 a Jigawa bayan tashe tashen hankula a lokacin zanga-zanga

Ɗanmodi ya bayyana cewa za a sassauta dokar daga karfe 12:00 zuwa 2:30 na rana domin ba mutane damar zuwa Masallacin Jumu'a.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262