Tsohon Gwamna Ya Ci Mutuncin Ƴan Arewa, Ya Ce Yawan Haihuwa Ya Jawo Wahala a Mulkin Tinubu
- Ayodele Fayose ya soki wasu ƴan Arewa da suke yawan haihuwa ba tare da suna samun isassun kudin kulawa da ƴaƴansu ba
- Tsohon gwamnan jihar Ekiti ya bayyana cewa hakan karawa gwamnati nauyi ne wadda a yanzu take kokarin tsayawa da kafafunta
- Fayose ya faɗi haka ne a wata hira da aka wallafa bidiyon a soshiyal midiya kan halin wahala da tsadar rayuwar da ake ciki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ekiti - Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya caccaki ƴan Arewa saboda yawan haihuwa ba tare da ɗaukar nauyin ƴaƴan ba.
Ayi Fayose ya bayyana cewa ya ziyarci wata jiha a Arewa, inda ya haɗu da mutane masu ƴaƴa rututu da mata huɗu kuma ba su da wata hanyar samun kuɗi.
Tsohon gwamnan ya yi wannan furucin ne a wata hira da Channels tv wadda aka wallafa a manhajar X da aka fi sani da Tuwita.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da aka tambaye shi kan hanyar da za a bi a magance tsadar rayuwa, Ayodele Fayose ya ba da labarin yadda ya tattauna da wasu mutane a lokacin da ya kai ziyara Arewa.
Ayo Fayose ya caccaƙi ƴan Arewa
"Akwai wata jiha ɗaya a Arewa, ba na son ambatar sunan jihar amma na kai ziyarar da na shafe kwanaki uku. A lokacin na tattauna da mutum ɗaya zuwa biyu."
"Na tambayi na farko ya faɗa mani N35,000 yake samu a wata amma yana da mata huɗu da ƴaƴa 17. Haba dan Allah ta ya mai samun N35,000 zai haifi ƴaƴa 17? Haba!
"Wani mutumin kuma ya faɗa mun yana da yara takwas da mata uku, ɗaya daga cikin matansa ma tana da juna biyu, don menene mutane za su riƙa haifar ƴaƴa barkatai su kara wa gwamnati nauyi?"
- Ayodele Fayose.
Fayose ya ce gwamnati na kokarin zama da kafafunta amma wasu ƴan Arewa suna haihuwa barkatai suna ƙara ɗora mata nauyi.
Gwamnan Kano ya gayyaci masu zanga-zanga
A wani rahoton kuma, Gwamma Abba Kabir Yusuf ya ce gwamnatinsa ba za ta lamunci duk wani abu da zai tada hankula ba a lokacin zanga zanga a Kano.
Gwamnan da aka fi sani da Abba Gida Gida ya kuma gayyaci masu shirin yin zanga-zangar domin su zo gidan gwamnatin Kano su tattauna kan kokensu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng