Ganduje Ya Yi Kamu, Babban Jigon da Ya Yaƙi Tikitin Musulmi da Musulmi Ya Koma APC

Ganduje Ya Yi Kamu, Babban Jigon da Ya Yaƙi Tikitin Musulmi da Musulmi Ya Koma APC

  • Yayin da jam'iyyu ke shirin tunkarar zaɓen 2027, Labour Party mai hamayya ta rasa ɗaya daga cikin manyan jiga-jiganta
  • Kwamared Isaac Balami, tsohon shugaba a kwamitin kamfen Peter Obi ya fice daga jam'iyyar LP zuwa jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya
  • Balami ya bayyana cewa ya yi tunanin LP ce warakar Najeriya amma shekara ɗaya da hawan Bola Tinubu mulki sai tunaninsa ya sauya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Matashin ɗan siyasa kuma masanin harkokin jirgin sama, Kwamared Isaac Balami ya sauya sheƙa daga Labour Party zuwa jam'iyyar APC mai mulki.

Balami, tsohon mataimakin manajan kwamitin yaƙin neman zaben Obi/Datti a zaɓen 2023 ya sanar da hakan a wata hira da manema labarai a Abuja ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya Sake ɗauko mace, ya naɗa ta a shirgegen mukami a gwamnatin tarayya

Peter Obi da Isaac Balami.
Kwamared Isaac Balami ya sauya sheka daga LP zuwa APC Hoto: Mr Peter Obi, Isaac Balami
Asali: Facebook

Kamar yadda The Nation ta ruwaito, Balami ya tuna yadda ya watsar da jam'iyyar APC gabanin zaɓen shugaban kasa a watan Fabrairu, 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa bayan tsawon lokaci ya sake nazarin matakin da ya ɗauka sa'ilin da ya ga jam'iyyar LP ta hargitse, rahoton This Day.

Balami ya faɗi dalilin komawa APC

Kwamared Balami ya ce gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta ba shi mamaki shekara ɗaya tal da fara mulki, bisa haka ya dawo APC.

Ya ce daman tikitin musulmi da musulmi shi ne babban dalilin da ya tsallaka zuwa jam’iyyar LP amma yanzu ya ga cewa a zahiri ba komai hakan yake nufi ba.

Isaac Balami ya ce:

"Zuwa yanzu Bola Tinubu ya naɗa Kiristocin Arewa da musulmai na ƙabilu daban daban a muƙaman gwamnati, tun da demokuraɗiyya ta dawo ba abin da ke burge ni face daidaito da adalci."

Kara karanta wannan

Ganduje ya sa labule da minista da manyan ƙusoshin APC a Abuja, an gano dalilin zaman

Matashin ɗan siyasar ya ƙara da cewa ba a taɓa shugaban ƙasar da ya jawo ƴan Arewa ta Tsakiya cikin gwamnatinsa kamar Bola Tinubu ba.

Balami ya kuma jinjinawa shugaban ƙasar bisa yadda gwamnatinsa ke zuba ayyukan alheri ciki har da naɗa ƴan Najeriya masu kishin ƙasa da son adalci.

Ganduje ya gana da jiga-jigan APC

A wani rahoton kuma jam'iyyar APC karkashin Dr. Abdullahi Umar Ganduje ta ci gaba da shirye-shiryen yadda za ta karɓe mulkin wasu jihohi a Kudu maso Gabas.

Abdullahi Ganduje, Sanata Ifeanyi Ubah da wasu manyan kusoshin APC daga jihar Anambra sun gana a wani Otal da ke birnin tarayya Abuja a ranar Laraba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262