Jam'iyyar APC Ta Dauki Muhimmin Mataki Bayan Ta Fuskanci Matsala
- Jam'iyyar APC a jihar Zamfara ta fara yunƙurin magance matsalar rikicin cikin gida da take fama da shi a jihar
- Jam'iyyar ta fara gudanar da taro duk wata-wata domin ɗinke ɓarakar da take fama da ita tare da haɗa kan mambobinta
- Tarurrukan waɗanda ake yi a dukkanin ƙananan hukumomin jihar na samun halartar masu ruwa da tsaki da shugabannin jam'iyyar daga kowane mataki
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Zamfara - Jam’iyyar APC reshen jihar Zamfara a ƙarƙashin jagorancin Tukur Danfulani, ta fara shirin ɗinke ɓarakar da take fama da ita.
Jam'iyyar ta fara ƙoƙarin magance matsalar rikicin cikin gida wanda yake barazana ga haɗin kanta.
Wane mataki APC ta ɗauka a Zamfara?
Jam’iyyar ta APC ta ƙaddamar da wani taro na wata-wata da ke ƙoƙarin haɗa kan dukkanin ƴaƴanta domin zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya, cewar rahoton tashar Channels tv.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wata sanarwa da sakataren yada labaran jam’iyyar Yusuf Idris ya fitar, ta ce taron na gudana ne a dukkanin ƙananan hukumomin jihar 14, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.
Taron na samun halartar dukkanin masu ruwa da tsaki, da kuma shugabannin jam’iyyar na jiha da na ƙananan hukumomi, mazaɓu, matasa da mata.
A karamar hukumar Gusau taron ya gudana a ƙarƙashin jagorancin Tukur Danfulani, yayin da a Kaura Namoda da Birnin Magaji ya samu halartar tsohon shugaban jam’iyyar Lawali Liman da sakataren jam’iyyar na jiha Ibrahim Dangaladima.
"Taron ya yaba da gudunmawar da jiga-jigan jam'iyyar suka bayar musamman ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle da Sanata Abdul'aziz Yari da sauransu."
"Shugabannin jam'iyyar da wakilansu sun kuma yi duba kan matsalar rashin tsaron da ta addabi jihar Zamfara da yankin gaba ɗaya, da sauran batutuwa masu muhimmanci."
- Yusuf Idris
Mambobin PDP sun koma APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar APC mai mulki ta samu ƙaruwa a jihar Benue yayin da manyan jam'iyyu suka fara shirin tunkarar zaɓen shekarar 2027.
Dubban mambobin jam'iyyar PDP waɗanda suka kai kimanin 4,450 sun watsar da tafiyar laima, sun koma jam'iyyar APC ranar Talata.
Asali: Legit.ng