Za a Yi Jana'izar Gwamnan APC da Ya Rasu a Kan Mulki, Sanarwa Ta Fito

Za a Yi Jana'izar Gwamnan APC da Ya Rasu a Kan Mulki, Sanarwa Ta Fito

  • Iyalan marigayi tsohon gwamnan jihar Ondo sun fitar da sanarwa kan shirye-shiryen jana'izar Rotimi Akeredolu
  • Bayan kammala duk wasu tarukan addu'o'i da bankwana, za a yi wa Akeredolu jana'iza a binne shi ranar 23 ga watan Fabrairu
  • Ranar Laraba, 27 ga watan Disamba, 2023, Gwamna Akeredolu na Ondo ya cika yana shekara 67 a duniya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ondo - Za a yi jana'izar marigayi tsohon gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu a mahaifarsa Owo, hedikwatar karamar hukumar Owo a jihar ranar 23 ga Fabrairu, 2024.

Iyalan marigayi gwamnan ne suka tabbatar da haka a wata sanarwa da ɗansa, Rotimi Akeredolu Jnr, ya fitar kuma aka wallafa a shafin Facebook.

Kara karanta wannan

Ana jita-jitar Kwankwaso zai sauya sheƙa, wani gwamna ya gana da jiga-jigan APC, ya buƙaci abu 2

Marigayi Rotimi Akeredolu.
Iyalai Sun Bayyana Ranar da Za a Yi jana'izar Marigayi Tsohon Gwamnan Ondo Hoto: Rotimi Akeredolu
Asali: Facebook

Marigayi Akeredolu ya rasu yana da shekaru 67 a ƙasar Jamus ranar Laraba, 27 ga Disamba, 2023, bayan ya yi fama da cutar kansa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Iyalai sun tura sako ga abokai da masu fatan alheri

Tsohon sakataren watsa labaran marigayi tsohon gwamnan, Mista Richard Olatunde, ne ya wallafa sanarwar jana'izar a shafinsa ranar Litinin.

Sanarwan ta ce:

"Iyalan Akeredolu na miƙa sakon godiya mara adadi ga dukkan waɗanda suka nuna mana kauna da tausayawa a daidai wannan lokaci mai matuƙar wahala bayan rasuwar Arakunrin Oluwarotimi Akeredolu, tsohon gwamnan Ondo.
"Ga wadanda suka dauki lokaci suka ziyarce mu a Ibadan da Owo, muna mika godiyarmu gare ku, zuwan ku ya ƙara mana kwanciyar hankali a zukatanmu, sannan nuna mana ana tare ya kara karfafa mu.
"Muna gayyatar ƴan uwa, abokai da masu fatan alkairi da su zo mu haɗu mu yi wa marigayi mai gidanmu bankwana da jana'izar da ta dace da shi.

Kara karanta wannan

A karon farko a tarihi, mace ta zama shugabar ƙaramar hukuma bayan lashe zabe a jihar arewa

Yadda za a yi jana'izar tsohon gwamna

Bikin ɓinne marigayi tsohon gwamnan zai shafe tsawon mako guda kuma za a gudanar da bukukuwan ne a garuruwan Ibadan, Akure da kuma Owo.

Za a yi hidimar jana'izar ne a Cocin St. Andrew's Anglican, Owo, sannan kuma a ɓinne shi a ranar 23 ga Fabrairu, 2024.

An kama masu hannu a yunkurin kisan shugaban majalisa

A wani rahoton kuma Jami'an hukumar ƴan sandan Najeriya su kama mutum biyu da ake zargi da hannu a yunƙurin kisan kakakin majalisar Benue.

Mai magana da yawun yan sandan ya bayyana cewa daga cikin waɗanda aka kama har da shugaban ƙaramar hukuma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262